APC Ta Mayarwa Sule Lamido Martani: Har Yanzu Kura-Kuren PDP Muke Gyarawa

APC Ta Mayarwa Sule Lamido Martani: Har Yanzu Kura-Kuren PDP Muke Gyarawa

  • Jam'iyyar APC ta yi martani ga tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, kan kalubalantar ci gaba da gwamnatin APC ta kawo a Najeriya daga 2015
  • Sule Lamido ya ce ba abin azo a gani da gwamnatin Tinubu da ta tsohon shugaban kasa Buhari suka yi wa 'yan Najeriya, yana mai cewa sun gaza
  • Sai dai, APC ta ce har yanzu tana gyara kura-kuran da PDP ta tafka a tsawon mulkinta na shekaru 16, da suka shafi cin hanci da rashawa da kama karya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ta yi martani ga tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, kan ikirarinsa na cewar jam'iyyar ta gaza.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-jigan APC da wasu da su ka caccaki Buhari kan jinginar da rubabbiyar gwamnati ga Tinubu

A karshen makon da ya gabat ne Lamido ya kalubalanci gwamnatin Tinubu da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na jefa Najeriya cikin mawuyacin hali.

Ganduje/Sule Lamdio
APC ta ce har yanzu tana gyara kura-kuran da PDP ta tafka a tsawon mulkinta na shekaru 16. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje/Mustapha Sule Lamido
Asali: Facebook

Cin hanci da rashawa suka mamaye mulkin PDP na shekaru 16 - APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi nuni da cewa daga shekarar 2015 zuwa yanzu, babu wani abin azo a gani da gwamnatin APC ta yi a kasar, inda ya ce mulkin PDP ya zarce na gwamnatin Buhari da Tinubu.

Sai dai a martanin da ta yi, jam'iyyar APC ta ce har yanzu tana kan gyara kura-kuran da jam'iyyar PDP ta tafka na tsawon shekaru 16 da ta yi a mulki, The Leadership ta ruwaito.

Mataimakin sakataren watsa labarai na APC na kasa, Duro Meseko ya ce cin hanci da rashawa, rashin alkibla suka mamaye mulkin PDP na shekaru 16.

Kara karanta wannan

Kano: Sakaci da dokar zabe ya jefa Gwamna Abba da NNPP cikon matsala, Kungiya ta bayyana

Muna gyara kura-kuran da PDP ta tafka a shekaru 16 - APC

Ya yi nuni da cewa da ace babu adalci a kalaman Lamido la'akari da irin ayyukan da gwamnatin APC ta shimfida sabanin yadda kasar ta lalace karkashin PDP.

A cewarsa:

"Bai kamata Sule Lamido ya manta cewa 'yan Najeriya ne da kansu suka kori PDP daga mulki a 2015 saboda neman mafita kan mulkin kama karya da ake yi masu.
"Ina so tsohon gwamnan Jigawa ya lura da cewa, gwamnatin APC ta dukufa wajen dawo da martabar Najeriya daga kura-kuran da PDP ta tafka lokacin da ta ke mulki."

Meseko ya ba 'yan Nigeria tabbacin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauki matakai masu tsauri don bunkasa tattalin arziki da kai kasar mataki na gaba.

SERAP ta bukaci Bankin Duniya ya daina ba jihohin Najeriya bashi

A wani labarin, kungiyar SERAP ta bukaci Bankin Duniya da ya dakatar da ba jihohin Najeriya rancen kudi kan zargin almubazzaranci.

Kungiyar ta ce babu abin da jihohin kasar ke yi sai aukin karbar bashi amma babu wani aikin azo a gani da ake yi da kudaden, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel