Kotun Zabe Ta Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Filato

Kotun Zabe Ta Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Filato

  • Kotun zaben yan majalisar jiha da ke zama a Jos, ta tsige kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Hon Moses Sule
  • Kotun ta kuma kwace kujerar dan majalisa mai wakiltan mazabar Jos ta arewa maso yamma a majalisar, Danjuma Azi
  • Ta mika nasarar zaben ga yan takarar jam'iyyar APC kan hujjar cewa PDP bata cancanci tsayar da dan takara ba saboda ba ta da tsari a jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Plateau - Kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin jiha da ke zama a Jos, babban birnin jihar Filato, ta tsige Hon Moses Sule, kakakin majalisar dokokin jihar.

An tsige kakakin majalisar, wanda ya kasance dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), tare da Danjuma Azi, dan majalisa mai wakiltan mazabar Jos ta arewa maso yamma a majalisar, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna: "Babu Wani Rudani a Hukuncin da Kotu Ta Yanke" Gaskiya Ta Bayyana

Kotun zabe ta tsige mambobin PDP biyu a majalisar dokokin jihar Filato
Kotun Zabe Ta Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Filato Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Kotu ta kwace kujerun yan majalisar PDP ta bai wa APC a jihar Filato

Kotun ta ayyana tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar, Hon. Naanlong Daniel da Hon. Mark Na’ah, dukkansu yan jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a matsayin wadanda suka lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wadanda suke kara sun kalubalanci daukar nauyin Sule da Azi kan hujjar cewa PDP bata cancanci shiga zaben ba saboda jam'iyyar bata da tsari.

PDP bata da tsari a jihar Filato

Da take zartar da hukunci, kotun zaben karkashin jagorancin Muhammad Tukur ta ce PDP bata cancanci daukar nauyin wadanda ake kara don zaben ba.

Ya riki cewa kamar yadda jam'iyyar bata da tsari, "babu abun da zai iya tsayawa a kan babu."

Da take soke zaben kakakin majalisar, kotun ta kuma umurci hukumar INEC da ta janye takardar shaidar cin aben da ta ba shi sannan ta mika shi ga Daniel Nanlong na APC wanda ya zo na biyu a zaben, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Uba Sani: Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Zabe Ta Yanke a Jihar Kaduna

Kotun zaben ta kuma bayyana cewa PDP ta ki bin umurnin Mai shari'a S P Gang na babbar kotun jihar Filato wanda aka yanke a ranar 26 ga watan Nuwamban 2020 wanda ya umurci jam'iyyar da ta gudanar da taron gundumomi.

Mai shari'a Tukur ya ce hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ki gabatar da kowace sahihiyar takarda da ke nuna cewa jam’iyyar ta sake yin taron a 2021, kamar yadda wadanda ake kara suka yi ikirari.

Babu rudani kan hukuncin kotun zaben gwamnan Kaduna, Uba Sani

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnan jihar Kaduna kuma dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben ranar 18 ga watan Maris, Uba Sani ya ce babu wani rudani a hukuncin kotun zabe na ranar Alhamis, wacce ta kori karar jam'iyyar PDP da Isah Ashiru kan nasararsa.

Sani ya bayyana hakan ne yayin hira da Channels TV a shirin Politics Today a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel