Daniel Bwala Ya Caccaki Wike Kan Barazanar Yin Rusau a Abuja

Daniel Bwala Ya Caccaki Wike Kan Barazanar Yin Rusau a Abuja

  • Daniel Bwala, kakakin Atiku Abubakar, ya caccaki barazanar yin rusau da sabon ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi
  • Wike bayan an rantsar da shi a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, ya sha alwashin tsaftace birnin Abuja da kuma rushe duk gine-ginen da ke ba bisa ƙa'ida ba, ko na waye kuwa
  • Sai dai, Bwala ya buƙaci tsohon gwamnan na jihar Rivers da ya mayar da hankali wajen abubuwan da za su amfani mazauna birnin ba ƙoƙarin kawo hargitsi ba

FCT, Abuja - Daniel Bwala, sanannen lauya kuma hadimin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyr Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya buƙaci ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da ya bi sannu a hankali.

Idan za a iya tunawa dai, Wike ya sha alwashin rushe gidajen da aka gina ba bisa ƙa'ida ba a babban birnin tarayyar, ba tare da la'akari da wanda za ta shafa ba.

Kara karanta wannan

FCT: Shehu Sani Ya Fadi Rigimar Da Wike Zai Janyowa Kansa Da Tinubu Idan Ya Ƙi Bi a Hankali

Daniel Bwal ya ja kunnen Wike
Daniel Bwala ya soki Wike kan yin rusau a Abuja Hoto: @BwalaDaniel, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Twitter

Bwala ya ja kunnen Wike

Da yake yin martani a kan hakan, Bwala a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya a ka sani da Twitter), a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, ya buƙaci Wike da ya shiga taitayinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bwala ya yi nuni da abubuwan da mazauna birnin tarayyar suka fi so, waɗanda yakamata tsohon gwamnan ya mayar da hankali a kansu.

Da yake tunatar da Wike cewa Abuja ba jihar Rivers ba ce, Bwala ya yi nuni da cewa idan jigon na jam'iyyar PDP ya kawo hargitsi a birnin, tabbas zai rasa muƙaminsa.

Bwala ya rubuta cewa:
"Zuwa ga wanda ta shafa"
"Barka yallaɓai, idan kana buƙatar a tunatar da kai, buƙatun da mazauna birnin tarayya Abuja su ke da su sune, ingantattun wuraren kiwon lafiya, samun wuraren karatu, wuraren wasanni da shaƙatawa masu kyau, hanyoyin yin sufuri masu arha, fitilun tituna masu kyau a birnin da wajensa, sannan daga ƙarshe kuma, tsaro."

Kara karanta wannan

FCT: Nyesom Wike Ya Bayyana Babban Dalilin Da Ya Sa Ya Karbi Minista a Gwamnatin Tinubu

"Ka zo da soki burutsu kana maganar rusau da ƙwace filaye. Abuja ba Fatakwal ba ce. Idan ka kawo hargitsi a birnin, za ka lalata kasuwar wanda ya naɗa ka muƙamin, ta yadda dole zai sanya ka rasa muƙaminƙa. Za ka fahimci ƙanƙan da kai a yayin aikin."

Fintiri Ya Taya Wike Murna

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya taya Nyesom Wike murnar zama ministan birnin tarayya Abuja.

Gwamnna ya bayyana cewa Wike ya cancanci zama minista bisa irin ayyukan da ya gudanar lokacin da yake kan kujerar gwamnan jihar Rivers.

Asali: Legit.ng

Online view pixel