Jigon APC Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Murkushe Arewa Tun Wajen Nada Ministoci
- Shehu Usman Modibbo ya jawowa mutane shakku game da mutanen da ake so su zama Ministoci
- Farfesan ya na cikin jagorori na jam’iyyar APC a Kaduna kuma ya na nuna kishin Arewacin Najeriya
- Akwai masu ra’ayinsa, su na zargin Bola Tinubu bai zakulo Ministocin da su ka dace daga Arewa ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kaduna - Da alama mutane irinsu Shehu Usman Modibbo ba su gamsu da mutanen da Bola Ahmed Tinubu ya dauko domin su zama Ministoci ba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a Twitter a ranar Laraba, Farfesa Shehu Usman Modibbo ya jefa alamar tambaya ga gwamnatin Bola Tinubu.
Watakila Farfesan cututtukan wanda ya saba nuna damuwarsa kan abin da ya shafi ‘Yan Arewa ya na cikin masu ganin ba a dauko kwararru ba.
Martanin mutanen Arewa a Twitter
Yayin da wasu su ke ganin jagoran na APC a jihar Kaduna ya yi gaskiya, an kuma samu masu maida masa martani cewa ba haka abin yake ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Modi Abba ya ce a shekaru takwas da su ka wuce, ‘Yan Arewa su ka hana kan su cigaba.
Hakan ya jawo wani Injiniya ya ce ko a gwamnatin Muhammadu Buhari, Farfesa Isa Pantami ne kurum wani kwararre daga Arewa a Ministoci.
A cewar Real Oil Sheikh, a maimakon a dauki irinsu Abdulrahman Dambazzau, sai aka zakulo Ibrahim Geidam, Bello Matawalle da sauransu.
Wasu su ka ce an yi haka ne da gangan saboda a raunata mutanen Arewacin Najeriya a gwamnati, sai dai yankin ne ya fi samun mukamai.
Da yake magana a Twitter, Injiniya Adam Hayatu ya ce daga Kudu an dauko kwararru da su ka san aiki, da aka zo Arewa an ga akasin hakan.
Babu wadanda su ka san aiki daga Arewa?
Daga yankin na Arewa ne Bola Tinubu ya dauko Farfesa Ali Pate, Nasir El Rufai, Arch. Ahmed Dangiwa, Hannatu Musawa da Farfesa Tahir Mamman.
Mohammed Idris Malagi, Imaan Suleiman Ibrahim, Yusuf Tuggar, Alkali Ahmed da Abubakar Kyari duk su na cikin Ministocin da aka tantance.
Wani kuma ya tunawa Farfesan da aka fi sani da Danfulani cewa Tinubu ya ba mutane irinsu Hadiza Bala Usman da Salma Kolo mukamai.
Wadanda ba su da rabon Minista
A baya mun tattaro maku sunayen manyan ‘yan siyasa daga Kudu da Arewacin Najeriya da Bola Tinubu ya manta da su wajen nada Ministoci.
Akwai ‘yan siyasar Kano; Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje su ka rasa mukaman, sannan akwai ‘yan kwamitin yakin neman zabe.
Asali: Legit.ng