Tinubu na Kaduna, El Rufai Ya Jefa Masa Tambayoyi 12, Ya Tuna Masa Hadisin Manzo
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya gabatar da tambayoyi 12 da yake son Shugaba Bola Tinubu ya amsa yayin gangamin APC a Kaduna
- El-Rufai ya tambayi Tinubu kan cire tallafin man fetur, matsalar tsaro, talauci, rashin wutar lantarki da karancin ayyukan yi a Najeriya
- Ya kuma bukaci shugaban ya bayyana matakan da ya dauka wajen farfado da masana’antu, inganta noma da cika alkawuran da ya yi wa al’ummar Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ƙalubalanci Bola Tinubu yayin da yake shirin kamfen a Kaduna.
El-Rufai ya ce jam’iyyar APC za ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na 2027 a Kaduna, saboda haka akwai tambayoyi da ya kamata ya amsa.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a yau Asabar 24 ga watan Oktobar shekarar 2026 da muke ciki.
El-Rufai ya ce wannan zai zama wani gangami, taron jama’ar da aka yi hayar su da kuma sababbin alkawuran da ba za a cika ba.
Ya ce hakan ya yi kama da gasar karya, inda mai magana ya san yana karya, masu sauraro sun san yana karya, amma dukansu suna nuna kamar ba su sani ba.
Sai dai ya cr a wannan karon, ya kamata tambayoyin su biyo ayarin motocin shugaban, kuma ya kamata a yi su ba ga wanda ke kan dandamali kadai ba, har da duk wanda ya hau dandalin, da kuma kowane dan Najeriya ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ba.
Ga tambayoyin El-Rufai 12 masu sauki kamar yadda ya rubuta:
1. Wane ne ya cire tallafin man fetur, kuma ina kudin da aka tara?
El-Rufai ya ce Kakakinsa, ciki har da Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben ku, Sanata Abdulaziz Yari, yanzu suna ikirarin cewa babu tanadin tallafin man fetur a kasafin kudin shekarar 2023 lokacin da kuka zama shugaban kasa.
Amma a daya bangaren, magoya bayanku suna bayyana cire tallafin a matsayin babbar nasarar ku.

Kara karanta wannan
Tinubu: Nasir El Rufai ya daura bidiyon abin da Sarkin Katsina ya fada wa Abdulaziz Yari
A ranar 29 ga Mayu, 2023, ka bayyana cewa Tallafin man fetur ba zai iya ci gaba da halatta hauhawar kudin da ake kashewa a kansa ba, musamman a lokacin da albarkatun kasa ke raguwa.
2. Tsaro: “Dan bindigar da ya tuba shi ne wanda ya mutu” — to, me ya sa ake tattaunawa da ’yan bindiga a Arewa, amma ba a Kudu maso Yamma ba?
A Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce dan bindigar da ya tuba shi ne wanda ya mutu.
Duk da haka, gwamnatinku na ci gaba da nazarin hanyoyin tattaunawa da bayar da afuwa ga ’yan bindiga a Arewa, yayin da take kin bin irin wannan hanya a yankin Yarbawa.
Me ya sa ake amfani da ma’auni biyu? Kuma mene ne ainihin matakan da kuka dauka domin dakile matsalar tsaro tun daga Mayun 2023?
3. “Ina wutar lantarki?” — gwajin da kuka sanya wa kanku na wa’adi na biyu
A lokacin yakin neman zaben 2023, kun yi alkawarin cewa idan kun kasa gyara matsalar wutar lantarki a Najeriya, kada ’yan Najeriya su sake zaben ku a shekarar 2027.
Ina wutar lantarkin? Shin samar da wutar lantarki ta kasa, karfin samar da ita ko rage kudin da ake biya sun inganta yadda za ku iya tsayawa kan wannan alkawari?
4. Talauci:
Hadimanka sun amince cewa talauci ta fuskoki da dama ya karu, kuma sama da kashi 75% na matalauta suna Arewa. Shin kun zo ne domin yi wa gwamnoni hisabi?
Bayo Onanuga da wasu kakakinka sun amince cewa talauci ta fuskoki da dama ya karu sosai.
Bayanai daga Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) sun nuna cewa sama da kashi 75% na mutanen da ke fama da irin wannan talauci a Najeriya suna Arewa.
5. Noma: Alkawarin Kaduna da matsalar karancin abinci
A ranar 12 ga Disamban 2022, a Kaduna, kun yi alkawarin cewa: “Za mu kafa hukumar kula da kasuwancin amfanin gona wadda za ta tabbatar muku da farashi mai kyau, ta samar muku da kwanciyar hankali a gidajensu, kuma ta inganta rayuwarku.”
Kun kuma yi alkawarin ba da fifiko ga noma domin tabbatar da wadatar abinci tun bayan hawanka mulki.
Tun daga wannan lokacin, hauhawar farashin abinci ta haura kashi 30% a mafi yawan shekarar 2024.
Daga baya, ta ragu zuwa kashi 10.84% a duk shekara zuwa Disamban 2025, musamman sakamakon sauya tsarin kididdiga da tasirin sabon ma’aunin kwatantawa.
Sauran tambayoyin sun hada da:
6. Ayyukan yi
7. Samar da masana’antu
8. Garkuwa da dalibai a Oyo da Borno
9. Sunday Igboho da sarakunan gargajiya na Arewa
10. Maganar tuhumar gwamnoni da laifi
11. Alkawauran gangamin Kaduna a 2022
12. Rashin cika alkawuran baya
El-Rufai ya a matsayin Tinubu na Musulmi, ya san karin maganar da ake dangantawa da Annabi Muhammad (SAW), wadda ke cewa mumini ba ya bari a cije shi daga rami daya sau biyu.
Alkawarin APC ga Tinubu a Kaduna
Kun ji cewa jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa za a samu dimbin magoya baya a bikin kaddamar da yakin neman zaben Shugaba Tinubu ranar Asabar a Kaduna.
Sakataren yada labaran APC na Arewa maso Yamma, Mailafiya Mada, ya ce an yi tanadin tsaro da kula da taron duk da karancin wurin taron.
Asali: Legit.ng


