Akume: Babba a Gwamnatin Tinubu Ya Bayyana Makiyan Arewa
- Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya ce duk ɗan Arewa mai neman shugabancin ƙasa a 2027 yana adawa da muradun yankin
- Akume ya ce an cimma yarjejeniyar karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu a Kaduna domin kiyaye haɗin kan Najeriya
- Ya yi kira ga ’yan Arewa da su goyi bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, su jira har zuwa 2031 kafin neman shugabancin ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya yi magana kan 'yan Arewa dangane da zaben 2027.
George Akume ya bayyana duk wani ɗan Arewa da ke neman takarar shugaban ƙasar Najeriya a zaɓen 2027 a matsayin maƙiyin yankin.

Source: Facebook
Akume ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoban 2026 yayin wani taron ganawa da ’yan asalin Jihar Benue da ke zaune a Kaduna, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Sakataren gwamnatin tarayyar ya buƙaci ’yan Arewa da su goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin samun wa’adi na biyu.
Jam’iyyar APC ta ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Kaduna a ranar Asabar ɗin.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), na daga cikin fitattun ’yan siyasar Arewa da ke ƙoƙarin kayar da Tinubu a zaɓen 2027.
Akume ya tuna da yarjejeniyar karɓa-karɓar mulki
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun SGF, Yomi Odunuga, ya fitar, an ruwaito Akume yana cewa an cimma yarjejeniyar karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu a Kaduna domin tabbatar da haɗin kan Najeriya.
Ya ce bai kamata a yi watsi da yarjejeniyar ba, domin tana daga cikin matakan da suka taimaka wajen ci gaba da kasancewar ƙasar a matsayin ɗaya, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Ku tuna cewa a wannan Kaduna ɗin ne muka amince da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu. Ba za ku yi shakkar cancantar mutanen da suka cimma wannan yarjejeniya a lokacin ba, domin an yi hakan ne don haɗa kan ƙasar nan.
“Mun amince da sauya ikon shugabanci tsakanin yankunan biyu, kuma wannan ne ya taimaka wajen ci gaba da tafiyar da ƙasar nan tare da kiyaye cikakken ikon Najeriya a kan yankunanta,” in ji shi.
“Lokacin Arewa zai zo a 2031”
Akume ya ce bai kamata wani ɗan Arewa ya nemi shugabancin ƙasa a 2027 ba, yana mai cewa lokacin yankin na komawa kan kujerar shugaban ƙasa zai kasance ne a 2031.
Ya buƙaci ’yan Arewa da kada su bari wani ɗan siyasa ya yaudare su su bijire wa abin da ya kira yarjejeniyar da aka cimma domin zaman lafiyar ƙasa.
“Duk wanda ya fito daga Arewa yana takarar shugaban ƙasa maƙiyin Arewa ne. Kada ku bari wannan mai surutun ya yaudare ku. Lokacinmu bai yi ba tukuna. Lokacin Arewa zai kasance a 2031. Ku shirya ku zaɓi Tinubu,” in ji Akume.
Ya kuma gargaɗi cewa bai kamata burin siyasar mutum ɗaya ya zama sanadin haddasa rarrabuwar kawuna ko kawo barazana ga haɗin kan Najeriya ba.

Source: Facebook
Shettima ya bukaci Arewa ta zabi Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya mika kokon bararsa ga masu zabe a yankin Arewacin Najeriya.
Shettima ya buƙaci su haɗa kai wajen mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Asali: Legit.ng


