Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni a Katsina, Ya Raba Ma'aikatar Ilimi

Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni a Katsina, Ya Raba Ma'aikatar Ilimi

  • Gwamnan Katsina ya rantsar da sabbin kwamishinoni 20 da kuma mashawarta na musamman 18 ranar Talata, 1 ga watan Agusta, 2023
  • Malam Dikko Raɗɗa ya tabbatar da cewa dukkan kwamishinonin mutanen mazabarsu ne suna zaɓi a naɗa su
  • Radda ya kuma raba ma'aikatar ilimi zuwa gida biyu, ma'aikatar ilimi mai zurfi, fasaha da aikin yi da kuma ma'aikatar ilimin tushe da Sakandire

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a ranar Talata, ya rantsar da sabbin kwamishinonin da majalisar dokokin jihar ta tantance tun farko.

Babban mai taimaka wa gwamna kan harkokin digital midiya, Isah Miqdad ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Gwamna Dikko yayin rantsar da kwamishinoni.
Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni a Katsina, Ya Raba Ma'aikatar Ilimi Hoto: @Miqdad_jnr
Asali: Twitter

Bayan haka, gwamna Raɗɗa ya bai wa sabbin mashawarta na musamman guda 18 rantsuwar kama aiki a taron wanda ya gudana a filin wasan People Square ranar Talata.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Zai Raba Buhuna 36, 000 na Kayan Abinci Kyauta a Kowane Gari

A jawabin da ya yi a wurin bikin rantsarwan, Radda ya ce galibin sabbin kwamishinonin mutanen mazaɓarsu ne suka zaɓe su bisa cancanta da kuma amana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Raɗɗa ya ce:

“Mutane suna cewa masu rike da mukamai a gwamnatinmu masu basira/fasaha ne, ina tabbatar muku da cewa dukkansu masu fasaha ne da kuma ’yan siyasa saboda mutanen mazabarsu ne suka mika sunayensu don nada su."

Raɗda ya bukaci sabbin wadanda aka nada da su gudanar da ayyukansu da kwazo da jajircewa maimakon su riƙa binsa duk inda ya je domin gudanar da aikinsa.

Gwamna ya raba ma'aikatar ilimi

Bugu da ƙari, Malam Dikko Raɗda ya amince da raba ma'aikatar ilimi ta jihar Katsina a wata sanarwa da kakakinsa, Ibrahim Kaula, ya rattaɓa wa hannu.

Sanarwan ta yi bayanin cewa ma’aikatu biyu da za su bullo bayan raba ma’aikatar sun kunshi ma'aikatar ilimi mai zurfi, fasaha da sana'o'i da ma'aikatar ilimin tushe da sakandire.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: NSA Na Shugaba Tinubu Ya Sa Labule Da Gwamnoni 5 a Abuja, Sahihan Bayanai Sun Fito

Yayin da Legit.ng Hausa ta tuntuɓi ɗaya daga cikin kwamishinonin da suka karɓi rantsuwar kama aiki, Hom. Ishaq Shehu Dabai, ta wayar tarho, ba a same shi ba domin layinsa a kashe.

Sai dai mamban APC kuma makusancin kwamishinan, Aliyu Yusuf, ya shaida wa wakilinmu cewa gwamna Radɗa da gaske yake wajen ceto Katsina domin ya ɗauko mutanen da suka cancanta.

"Muna yaba wa mak girma gwamna, domin ya naɗa mutanen da suka cancanta masu hazaka da son ci gaban al'umma, a yanzu ko ɗan adawa ya san Dikko ya ɗauko hanyar gayara Katsina."
"Fatan mu Allah ya taimake su baki ɗaya kuma ya basu ikon sauke nauyin da ya hau kansu a matsayin shugabanni, Ameen," inji shi.

Kotu Ta Jingine Yanke Hukunci Kan Karar da Atiku Ya Kalubalanci Nasarar Tinubu

A wani rahoton na daban kuma Kotun sauraron karar zaben shugaban ƙasa ta fara shirye-shiryen yanke hukunci kan zaben da shugaba Tinubu ya lashe a 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: "Mun Tara Sama da N1tr" Shugaba Tinubu Ya Tona Kuɗin Da Ya Ƙwato Bayan Cire Tallafin Fetur

Kotun ta jingine yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ƙalubalanci nasarar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel