Majalisar Dattawa Ta Tantance Wike Domin Zama Minista a Gwamnatin Shugaba Tinubu

Majalisar Dattawa Ta Tantance Wike Domin Zama Minista a Gwamnatin Shugaba Tinubu

  • Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, ya samu anincewar majalisar dattawa domin ya zama ministan Shugaba Tinubu
  • Tsohon gwamnan ya sha alwashin cewa ba zai ba mara ɗa kunya ba idan ya fara aiki a matsayin minista a gwamnatin Bola Tinubu
  • Wike wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda Tinubu ya zaɓo domin ba su kujerar minista, ya bayyana a gaban majalisar ne domin a tantance shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta tantance tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, domin samun muƙamin minista a ranar Litinin, 31 ga watan Yulin 2023, rahoton The Punch ya tabbatar.

Wike bayan ya gama karanto muƙaman da ya taɓa riƙe wa da nasarorin da ya samu, ya yi nuni da cewa ƙaunar da yake yi wa Najeriya ce ta sanya ya amince ya karɓi tayin zama minista.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Hana Ministan Da Tinubu Ya Zabo Daga Rike Mukami? Lauya Ya Bayyana Gaskiya

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya kuma bayyana cewa ba zai ba Shugaba Tinubu kunya ba, a duk muƙamin da ya ba shi ya riƙe.

A kalamansa:

"Na amince na zama minista ne saboda son hidimtawa Najeriya da na ke da shi."
"Ina bayar da tabbacin cewa idan aka amince da naɗi na, duk muƙamin da shugaban ƙasa ya bani, ba zai yi nadamar naɗa ni ba."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanatocin Rivers sun goyi bayan Wike a majalisa

Tun da farko, Sanatocin dake wakiltar jihar Rivers a ƙarƙashin wakilcin Sanata Barinada Mpigi (PDP, Rivers ta Kudu maso Gabas) a lokacin tantancewar, ya gayawa ƴan Najeriya cewa, babu wanda ya kai Wike cancanta daga jihar Rivers.

"Mai girma tsohon gwamna Nyesom Wike ba mu da tamkarsa a jihar Rivers. Shugaban mu ne kuma abun koyi a gare mu." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Stella Okotete: Lauya Ya Bukaci Majalisa Ta Fatattaki Daya Cikin Ministocin Tinubu, Ya Bada Kwakkwaran Dalili

"Ƴan uwa na Sanatoci, mu na buƙatar ku da ku bari kawai ya yi gaisuwa ya tafi."

Daga nan sai shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya gaya masa cewa ya yi gaisuwa kawai ya tafi.

Wanda Tinubu Zai Ba Minista Daga Jihar Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mai sharhi kan harkokin siyasa ya zayyano mutanen da Shugaba Tinubu zai iya ba muƙamin minista daga jihar Kano.

MS Ingawa ya yi tsokaci cewa akwai mutum biyar waɗanda a cikinsu ne Shugaba Tinubu zai ɗauki ɗaya ya ba shi muƙamin minista. Cikin mutanen akwai Rabiu Musa Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel