Yadda Bincike da Zargin Sata Zai Jawo Na Hannun Daman Tinubu Su Rasa Ministoci

Yadda Bincike da Zargin Sata Zai Jawo Na Hannun Daman Tinubu Su Rasa Ministoci

  • Bola Ahmed Tinubu zai iya bada mamaki a lokacin da ya fitar da wadanda za su zama Ministoci
  • Za a nemi sunayen wasu masu kusancin da shugaban kasar a rasa saboda zargin da yake wuyansu
  • Tinubu zai yi amfani da rahoton da jami’an tsaro da hukumomin tsaro su ka ba shi wajen kafa gwamnati

Abuja - Wasu ‘yan siyasa da ke tunanin kusancinsu da Bola Ahmed Tinubu zai jawo su samu kujerar Minista, za su sha mamaki ba da dadewa ba.

Wani bincike da Punch ta gudanar, ya nuna cewa shugaban kasa zai dogara da rahoton da jami’an tsaro su ka gabatar masa wajen nada Ministoci.

Hukumomin tsaro da na binciken rashin gaskiya za su iya kawowa wasu daga cikin wadanda Bola Tinubu ya mika sunayensu domin samun mukami.

Kara karanta wannan

Majiya Ta Bayyana Wanda Tinubu Zai Iya Nadawa a Matsayin Ministan Kudi

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a taron AU Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ina makomar tsofaffin Gwamnonin APC?

Wata majiya ta shaida cewa akwai Gwamnonin jihohin da su ka bar ofis a watan Mayu da sun ci burin samun kujera a sabuwar gwamnatin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika akwai ‘yan siyasa, sarakunan gargajiya, masana da ‘yan Najeriya da ke kasar waje da shugaban kasar yake tura sunayensu domin yin bincike.

A maimakon ya nada wadanda yake so kai tsaye, Mai girma Bola Tinubu zai saurari sakamakon binciken da aka gudanar, hakan zai sa ayi waje da wasu.

Binciken ya yi nisa, a sanadiyyar haka ‘yan siyasan da ake zargi da rashin gaskiya da wadanda aka samu da laifi za su girgiza da jin rahoton da ke kansu.

Rahoton ya ce a maimakon Tinubu ya yi watsi da ‘yan siyasar nan da ke kusanci da shi, zai yi amfani da binciken da hukumomi su ka yi, ya yi fatali da su.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Yan Najeriya 4 Da Suka Yi Aiki Da Buhari Kuma Suka Samu Sabbin Mukamai

Idan kuwa sun dage sai an ba su mukami, za su gamu da kalubale a majalisar dattawa yayin tantance su.

Za ayi waje da wasu jiga-jigai 2

Wata majiyar ta kara shaida cewa akwai tsofaffin Gwamnoni biyu da ake zargi da rashin gaskiya da ba za a mukami ba, duk da gudumuwar da su ka ba APC.

"Ku jira ku gani, wasu za su sha mamaki. Wasunsu za su nemi su koma ‘yan adawa domin su da mutanensu ba su cikin jerin Ministocin."

- Majiya

Ambode da 'yan adawa

Rahoton na Punch ya nuna Tinubu ya shirya farfado da siyasar tsohon Gwamnan Legas, Akinwumi Ambode wanda APC ta hana tikitin tazarce a 2019.

Watakila Tokunbo Abiru ya samu kujerar Minista, hakan zai ba Ambode damar tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Legas ta gabas a majalisar dattawa.

Tinubu ya shirya nada wasu daga ‘yan jam’iyyun APGA da NNPP a gwamnatinsa. Haka zalika ana tunanin zai tafi da wasu ‘Yan G5 da ke jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Jerin Shahararrun Yan Siyasa Da Suka Ki Amsar Tayin Zama Ministocin Shugaban Kasa Tinubu

...LP za ta iya samun Minista

An rahoto cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana so ya jawo cikas a jam’iyyar LP ta hanyar nada wani daga cikin mutanen Peter Obi a matsayin Ministoci.

Daniel Bwala ya ce daga cikin manyan ‘yan kwamitin yakin neman zaben Peter Obi akwai wanda aka yi wa tayin mukami kuma ya amince da maganar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel