Hadimin Atiku Ya Zargi Fayose Da Ziyartar Tinubu Don Janye Tuhumar Da EFCC Ke Masa

Hadimin Atiku Ya Zargi Fayose Da Ziyartar Tinubu Don Janye Tuhumar Da EFCC Ke Masa

  • Ana zargin tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da zawarcin Tinubu don ya sa a janye tuhumar da ake masa ta cin hanci da rashawa
  • Fayose dai ya daɗe yana fafatawa da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa (EFCC)
  • A kwanakin baya, an zarge shi da laifin cin hanci da rashawa na naira biliyan 1.7 wanda har yanzu ake ci gaba da shari'a a babbar kotun tarayya

Birnin tarayya Abuja - Mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar kan harkokin yaɗa labarai, Mista Phrank Shaibu, ya caccaki Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti, kan hirar da ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli.

A cikin hirar, Fayose ya bayyana cewa ya yaƙi takarar shugabancin ƙasa da Atiku ya yi wajen goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Da Gaske Wike ‘Karamin Mahaukaci Ne’? Hadimin Atiku Ya Yi Martani Ga Furucin Fayose

Hadimin Atiku ya zargi Fayose da nemawa dansa mukami wajen Tinubu
Hadimin Atiku ya zargi Fayose da neman mafaka daga EFCC wajen Tinubu. Hoto: @DavidsOffor
Asali: Twitter

Fayose ya goyi bayan Tinubu maimakon Atiku

Wannan ne karo na farko da Fayose ya bayyana goyon bayansa kai tsaye ga Tinubu gami da nuna adawarsa ga Atiku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu, Phrank Shaibu ya ce tun kafin zaɓe ya kamata a ce Fayose ya fito ya taya Tinubu yaƙin neman zaɓe.

Shaibu ya kuma bayyana cewa a shekarar 2022, Fayose ya bayyana a wajen wani taro cewa Atiku zai goyi baya duk da saɓanin da ya samu da Wike.

Ya ce jim kaɗan bayan sanar da cewa Tinubu ne ya lashe zaɓe, sai aka ji Fayose ya ɓara yana cewa shi ne ya kawowa Tinubu jihar Ekiti a zaɓen da ya gabata.

Ana zargin Fayose na neman a janye tuhumar da EFCC ke masa

Kara karanta wannan

Tinubu Nayi wa Aiki, Amma Ba Zan Karbi Tayin Minista ba – Tsohon Gwamnan PDP

A kwanakin baya, Fayose ya kai ziyarar ban girma zuwa ga shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa.

Shaibu ya ce Fayose duk yana yin waɗannan abubuwan ne don ganin Tinubu ya sa baki an dakatar da shari’arsa ta cin hanci da rashawa ta N1.7bn a babbar kotun tarayya.

Ya ƙara da cewa Fayose na ƙoƙarin samowa ɗansa muƙami ganin cewa ba zai sami muƙamin minista daga jihar Ekiti ba.

Wike ya yi nasara kan Atiku bayan da dan takararsa ya samu babban muƙami

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan Honarabul Kingsley Chinda, ɗan Majalisar Wakilai daga jihar Ribas, da ya yi nasarar samu kujerar shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya.

Wannan gagarumar nasara ce a wajen tsohon gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, da ya zamto ɗan tsaginsa ne ya samu wannan gagarumar nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel