Tinubu Ya Fadi Yadda Ya Soke Tsarin Buhari, Ya Hana a Auka CIkin Matsin Tattalin Arziki

Tinubu Ya Fadi Yadda Ya Soke Tsarin Buhari, Ya Hana a Auka CIkin Matsin Tattalin Arziki

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi bayanin hikimar daidaita farashin kasashen ketare da gwamnatinsa ta yi
  • Shugaban Najeriya ya ce kishin kasa ya jawo ya karya darajar Naira da nufin bunkasa tattalin arzikin kasa
  • Tinubu ya gabatar da jawabi wajen bikin da gwamnatin Legas ta shirya masa a kan darewarsa kan mulki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya kare kan shi daga zargin masu zargi a game da daidaita farashin kudin kasashen waje da gwamnatinsa ta yi.

This Day ta rahoto Shugaban kasar ya na wannan bayani a wajen bikin da gwamnatin jihar Legas ta shirya domin karrama shi a Marina.

Bola Ahmed Tinubu yake cewa ya dauki wannan mataki ne saboda kishin kasa, ya ce idan da ya so zai bari a cigaba da tafiya kan yadda aka saba.

Kara karanta wannan

Manyan Abubuwa 5 Da Shugaba Tinubu Ya Aiwatar a Watansa Na Farko a Ofis

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Legas Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Nufin ceto tattalin arzikin kasa

Shugaba Bola Tinubu ya ce zai fi amfana da tsarin da ya soke ta hanyar yin kudi da kasuwar canji, amma ya zabi ya ceto tattalin arzikin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake bayani a ranar Alhamis, jaridar ta ce Tinubu ya kamanta daidaita kudin kasashen ketare da cire tsarin tallafin man fetur da ya yi a baya.

"Zan iya amfana da moriyar ta hanyar shiga cikin badakalar, amma Allah ya tsare ni da haka! Ba abin da ya sa ku ka zabe ni ba kenan.
Dole mu dauki wadannan matakan domin kawo karshen matsalar tattalin arzikinmu ta daukar gaggawan mataki kan tallafin man fetur.

- Bola Tinubu

A rahoton da aka fitar a tashar talabijin ta Arise, an ji shugaban na Najeriya ya na cewa zai dage wajen ganin ana amfana da dukiyar da ke kasar.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Caccakar Emefiele, Ya Yi Batun Canza Naira Domin Hana Shi Cin Zabe

Tinubu ya kuma nemi goyon bayan Gwamnonin jihohi wajen kawo cigaba a Najeriya, ya ce akwai bukatar hadin-kai wajen bunkasa tattalin arziki.

A wajen wannan taro ne aka ji Tinubu ya godewa ‘ya ‘yan jam’iyyarsa da magoya bayan da ke tare da shi na tsawon lokaci har ya samu mulki.

Mai girma shugaban kasar ya ji dadin ganin tsohon Gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode wanda ya bar mulki da ya gagara samun tikiti a APC.

Fetur zai iya komawa N700

Daga N540, rahoto ya zo cewa fetur zai koma akalla N700 a yankin Arewa, za a dawo sayen lita a kan N600 a Legas idan kasuwar canji ba ta canza ba.

Wani ‘dan kungiyar IPMAN ya ce abin da ya ke hange shi ne mutanen Legas za su biya kusan N600 a duk lita saboda tsadar da Dalar Amurka ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel