Tinubu Ya Sake Caccakar Emefiele, Ya Yi Batun Canza Naira Domin Hana Shi Cin Zabe

Tinubu Ya Sake Caccakar Emefiele, Ya Yi Batun Canza Naira Domin Hana Shi Cin Zabe

  • Bola Ahmed Tinubu ya ce ko da an yi canjin takardun kudi daf da zabe, ya hango nasara a takararsa
  • Shugaban kasar ya soki tsarin da Godwin Emefiele ya kawo, a yanzu Gwamnan na CBN ya na tsare
  • Tinubu yake cewa ya fuskanci kalubale da yake neman takarar Shugaban kasa, a karshe ya zama tarihi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ogun - A jiya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya sa ran zai yi nasara a zaben 25 ga watan Fabrairu duk da wasu kalubale da ya fuskanta wajen takarar 2023.

This Day ta rahoto Bola Ahmed Tinubu ya soki tsarin canza kudi da babban bankin CBN ya kawo, shugaban kasar ya ce hakan bai hana shi yin nasara ba.

Shugaban Najeriyan ya yi wannan bayani ne da ya ziyarci Sarakunan Ijebuland da Egbaland; Oba Sikiru Adetona da Oba Adedotun Gbadebo a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Hadimin Wike Ya Dauki Zafi, Ya Fadi Abin da Ya Jawo Atiku Ya Fadi Zaben 2023

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a Legas Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya ce a Ogun ya fara da’awar “emi lo kan” da nufin cewa lokaci ya yi da zai yi mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An gamu da cikas a zaben 2023

Da yake bayanin wahalhalun da ya ci karo da su a zaben shugaban kasa, Tinubu ya ce an karbe dukiyoyin jama’a da sunan tsarin takaita yawon kudi.

Dele Alake ya fitar da jawabi, inda aka ji Mai girma shugaban kasar ya na sukar tsarin da Godwin Emefiele ya fito da shi a lokacin yana rike da CBN.

“An karbe mana kudi. Tsarin takaita yawon kudin bai yi aiki ba, abin bai yi kyau ba. Daga nan na ga bukatar zuwa Ogun domin yin kira ga neman ‘yanci da aka san mu da shi.

- Bola Tinubu

Baram-barama ko fadan gaskiya a Ogun

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya Yau, Akwai Yiwuwar a Nada Ministoci Bayan Sallah

Tinubu ya ke bayani a fadar Awujale cewa sau biyu ya na fitowa karara ya na yin kalamai baro-baro a Ogun lokacin da ake shirye-shiryen zaben 2023.

Da farko ‘dan takaran (a lokacin) ya yi jawabin 'Emi lo kan;, a karo na biyu ya ce ko an canza takardun Naira ko ba a canza ba, zai zama shugaban Najeriya.

Baya ga Sarakunan da su ka karbe shi, Punch ta ce Tinubu ya yi godiya ga shahararren attajirin kasar nan, Mike Adenuga wanda ya halarci taron.

Wadanda shugaban kasar ya yi godiya na musamman a kan kokarinsu a zaben bana sun hada da Oba Gbadebo, Aremo Olusegun Osoba da Dimeji Bankole.

Mai girma shugaban kasa ya godewa Ibikunle Amosun da shugaban APC na Ogun da su ka dage wajen kamfe duk da rashin kudi da wahalar fetur a lokacin.

Za a wangale iyakokin kasa

Alamu na nuna gwamnatin tarayya ta cire takunkumin da Muhammadu Buhari ya kakaba a baya na haramta shigo da motoci daga ketare da iyakokin kasa.

Kara karanta wannan

Buhari: Abin Da Ya Sa Na Bar Tinubu Da Aikin Cire Tallafin Man Fetur Idan Ya Hau Mulki

Rahoto ya zo cewa ana sa ran matakin ya farfado da tattalin arzikin garuruwan da ke kan iyaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel