Shugaban Makaranta ya Tsere da Kudin Jarrabawar WAEC da NECO, Ya Lula Kasar Waje

Shugaban Makaranta ya Tsere da Kudin Jarrabawar WAEC da NECO, Ya Lula Kasar Waje

  • Wasu dalibai a Ibadan da ke jihar Oyo sun ga ta kansu bayan shugaban makarantar da su ke zuwa ya cika wandonsa da iska da kudin jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO
  • Rahotanni sun bayyana cewa malamin ya sayar da kadarorinsa, sannan ya tattara abubuwan da ya mallaka ya bar Najeriya baki daya wanda ya sa iyayen su ka rasa madafa
  • Shugabar Planet 3R founder Adejoke Lasisi ta wallafa a shafinta na facebook cewa makarantar na kusa da gidanta, kuma da yawan iyayen yaran bashin kudin jarrabawar su ka ci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Oyo- Iyayen yara a jihar Oyo za su shiga wani hali bayan shugaban makarantar da yaransu ke zuwa ya cika wandonsa da iska da kudin jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO.

Kara karanta wannan

Harin masallacin Kano ya haifar da marayu da Zawarawa da dama

Rahotanni na zargin shugaban makarantar ya tattara dukkanin kudaden, sannan aka neme shi aka rasa kamar ya yi layar zana.

Makaranta
WAEC & NECO: Shugaban makaranta ya tsere da kudin jarrabawar dalibai a Ibadan Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Shugabar Planet 3R founder Adejoke Lasisi ta wallafa a shafinta na facebook cewa iyayen yaran sun shiga mawuyacin hali saboda rashin tabbas da jarrabawar yaransu ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyaye sun ci bashin kudin WAEC & NECO

Wasu iyaye da su ka ci bashin kudi domin biyawa yaransu kudin rubuta jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO a Ibadan sun shiga tsaka mai wuya.

Legit.ng ta ruwaito cewa iyayen sun fada halin ne bayan shugaban makarantar da yaransu ke zuwa ya gudu da kudin jarrabawar.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin ya tattare duk abin da ya mallaka, sannan ya sayar da gidansa kafin ya bar Najeriya.

Labarin wanda ya cinye kudin WAEC & NECO

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

A kalaman Shugabar Planet 3R founder Adejoke Lasisi:

"Wasu mutanen ba su tsoron Allah ko kadan, ya mutum zai karbi kudin jarrabawar WAEC/NECO sannan ya bar kasar.”
“Wannan abu ya faru a unguwarmu…wani mai makaranta…makarantar ta dade a yankin Amuro, Egbeda Ibadan.”
“Mai makarantar ya karbe kudin WAEC da NECO, wasu iyayen ma rance su ka yi domin yiwa yaransu rajistar jarrabawar.”

Adejoke Lasisi ta ce za ta bayyana sunan makarantar da mai ita nan gaba kadan.

An saka dokar ta-baci kan ilimi

A baya mun ruwaito mu ku cewa gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar ta baci a kan bangaren ilimi domin inganta shi a dukkanin sassan jihar.

Kwamishinan ilimi, Umar Haruna Doguwa ya bayyana haka inda ya ce bangaren ilimi a Kano ya fada cikin mawuyacin hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel