Bola Tinubu: Manyan Abubuwa 5 Da Shugaban Najeriya Ya Aiwatar a Watansa Na Farko a Ofis

Bola Tinubu: Manyan Abubuwa 5 Da Shugaban Najeriya Ya Aiwatar a Watansa Na Farko a Ofis

An rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu dai ne a matsayin shugaban Najeriya na 16 a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

A jawabinsa na farko a matsayin shugaban kasa, Tinubu ya yi wasu alkawura ciki har da alkawarin yin mulki domin amfanin ‘yan Najeriya.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi mulki a madadin 'yan kasa ne amma ba a kansu ba, kuma gwamnatinsa za ta yi shawara da tattaunawa a kan abubuwan da za ta aiwatar.

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar tun bayan hawansa mulki
Muhimman abubuwa 5 da Shugaba Tinubu ya yi tun bayan hawansa mulki. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya kuma ba da tabbacin cewa, zai tuntubi kowa da kowa don shawara, kuma ba zai riki wani a zuciya ba don ya saba da ra'ayinsa.

Kwanaki 30 kenan da hawansa karagar mulki, kuma akwai wasu matakai kwarara da Tinubu ya dauka, wasu daga cikinsu sun tada kura tare da janyo muhawara a tsakanin jama'a.

Kara karanta wannan

Ana Jiran Amincewar Shugaba Tinubu Wajen Ƙara Tsadar Wutar Lantarki a Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mun tattaro muku wasu biyar daga cikin muhimman abubuwan da Tinubu ya aiwatar a cikin watansa na farko kan karagar mulki, daga jaridar Daily Trust.

1. Cire Tallafin Man fetur

A ranar 29 ga watan Mayu, yayin da aka rantsar da shi, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ba za a sake samun tallafin man fetur ba saboda babu shi a kasafin kudi na shekarar 2023.

Sabon shugaban ya bayyana cewa za a karkatar da kudaden tallafin zuwa wasu muhimman bangarori irinsu ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi.

A wani mataki na gaggawa bayan sanarwar, gidajen mai da ‘yan kasuwa sun fara boye man fetur din, lamarin da ya janyo dogayen layuka a wasu gidajen mai da kuma dagawar farashin man.

'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan karin farashin man fetur da ya janyo hauhawar farashin kayayyaki da abubuwa da dama da kuma kara janyo tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Za Ta Samar Da Ayyuka Miliyan 1 Ga Matasan Najeriya, Kashim Shettima Ya Yi Bayani

2. Dakatar da gwamnan CBN, Emefiele

Kasa da mako biyu da hawansa mulki a matsayin shugaban kasa kuma babban kwamandan askarawan Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele daga mukaminsa.

A cewar wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar kuma ya sanyawa hannu, ta ce an dakatar da Emefiele ne don gudanar da bincike da kuma shirin yin garambawul a fannin kuɗi da tattalin arziƙi.

Daga baya kuma jami’an ‘yan sanda na farin kaya sun kama Emefiele, sa’o’i kaɗan bayan dakatar da shi.

Emefiele dai ya fuskanci suka ne sakamakon yadda ya shiga harkokin siyasa tsunduma musamman yadda ya nuna aniyarsa ta neman tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.

Ya kuma sha suka sosai daga yan Najeriya kan manufofin sake fasalin takardar kuɗin naira da kuma wahalhalun da hakan ya janyowa ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya Yau, Akwai Yiwuwar a Nada Ministoci Bayan Sallah

3. Dakatar da shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa

Haka kuma a cikin kwanaki 16 na farko na mulkin Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar da shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.

Wata ‘yar takaitacciyar sanarwa daga ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya, ta ce shugaban ya dakatar da Bawa ne bisa wasu manyan zarge-zarge na cin zarafin ofishinsa da ake yi masa.

A dai-dai wannan rana, hukumar DSS ta fitar da sanarwar a shafinta na Tuwita, cewa Bawa ya amsa gayyatar da aka yi masa domin gudanar da bincike.

4. Dakatar da shugabannin tsaro da naɗa wasu sabbi

A ranar 19 ga watan Yuni, shugaban kasa ya amince da yin murabus na gaggawa ga dukkanin shugabannin tsaro na soji, Sufeto-Janar na ‘yan sanda, masu ba da shawara, Kwanturola-Janar na kwastam daga aiki ba tare da ɓata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Wani Sojan Ruwa Ya Sharara Masa Mari a Amurka

Shugaban ya kuma bayyana sunayen waɗanda suka maye gurbinsu.

Hakazalika Tinubu ya naɗa Nuhu Ribadu a matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), mako guda da naɗa shi mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin tsaro.

5. Naɗin masu ba da shawara na musamman

A ranar 5 ga watan Yuni, Shugaba Tinubu ya naɗa wasu mashawarta na musamman guda takwas da suka haɗa da tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu wanda daga baya ya zama NSA.

Haka nan Tinubu ya nada tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Legas, Dele Alake a matsayin mai ba da shawara na musamman, da kuma Wale Edun, wanda tsohon kwamishina ne a Legas, da aka naɗa shi a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kuɗi.

Buhari ya musanta rahotan cewa ya nemi Tinubu ya dakatar da bincike kan mukarrabansa

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya musanta batun da ake yadawa cewa ya nemi Shugaba Tinubu ya dakatar da binciken da yake yi akan mukarrabansa.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Shugaba Tinubu Ya Faɗi Gaskiyar Yadda Ya Cire Tallafin Man Fetur Ranar Rantsarwa

Kakakin tsohon shugaban kasar, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel