Hasashen ‘Yan Kasuwa Ya Nuna Man Fetur Zai Iya Kai N700 a Jihohin Arewacin Najeriya

Hasashen ‘Yan Kasuwa Ya Nuna Man Fetur Zai Iya Kai N700 a Jihohin Arewacin Najeriya

  • Daga watan Yuli da za a shiga nan da ‘yan kwanaki, za a iya samun farashin man fetur ya canza
  • Wani ‘dan kasuwa ya ce farashin fetur zai haura N540 da aka saba saye yanzu a gidajen man kasar
  • Kudin zai danganta ne da farashin kudin kasashen waje a Najeriya da tsadar danyen mai a Duniya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - ‘Yan kasuwan mai sun yi hasashen cewa litar man fetur zai iya zarce N700 a jihohin Arewacin Najeriya daga watan Yulin nan da za a shiga.

Wani babban jami’in kungiyar IPMAN, Mike Osatuyi ya shaidawa Punch cewa farashin fetur zai tashi da zarar ‘yan kasuwa sun fara shigo da mai.

A watan gobe ne za a fara kawo mai Najeriya daga kasashen ketare. A lissafin da Mike Osatuyi yake yi, hakan zai jawo fetur ya kara tsada a Arewa.

Kara karanta wannan

Ana Jiran Amincewar Shugaba Tinubu Wajen Ƙara Tsadar Wutar Lantarki a Najeriya

Fetur
Gidan man fetur a Najeriya Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lissafin da IPMAN ta ke yi

A cewar ‘dan kasuwan, wadanda ke Legas za su rika sayen duk litar fetur a kimanin N600-N610. The Cable ta dauko wannan rahoto a ranar Laraba.

"Abin da na ke gani shi ne akalla N600, ya danganta da farashin kudin waje, farashin danyen mai a kasuwar Duniya da kuma kudin shigo da man.
Mutanen da ke Legas za su biya kusan N600, wadanda ke wajen Legas za su biya fiye da N600, wadanda ke Arewa za su rika saye fiye da N7000."

- Mike Osatuyi

NMDPRA ta na bada lasisi

Shugaba hukumar NMDPRA ta kasa, Olufemi Adewole ya shaidawa jaridar cewa a halin yanzu ana cigaba da bada lasisi domin shigo da mai daga waje.

Da zarar an shiga watan Yuli kuwa, Adewole ya ce kudin da za a saida fetur a gidajen mai ya danganta da yanayin kasuwa a lokacin da kudin kasashen waje.

Kara karanta wannan

Miliyan 1 Na Ke Ware Wa Jami'an Kan Hanya Yayin Jigilar Shanu Daga Arewa Zuwa Kudu, In Ji Isiaka

Shugaban na NMDPRA ya tabbatar da farashi zai iya tashi, amma ya kara da cewa akwai yiwuwar nan gaba ya sauko idan Naira ta yi daraja a kasuwar canji.

Baya ga haka, ‘yan kasuwa za su rika karya farashinsu da zarar sun fahimci ba su samun ciniki, masu shigo da fetur za su koma takara da junansu.

A dalilin daidaita kudin kasashen waje da bankin CBN ya yi, ‘dan kasuwa ya na bukatar sayen Dala kan N765 kafin ya tafi ketare ya shigo da mai.

Kudin lantarki zai bi na man fetur

Rahoto ya zo cewa kamfanin AEDC ya ce kudin shan wutar lantarki zai canza. Ana so a ƙara kuɗin sayen lantarki daga makon gobe saboda Dala ta tashi.

Kamfanin AEDC ya nuna abubuwa sun canza bayan Gwamnati ta canza tsarin tattalin arziki. Sai dai yin hakan zai sake jefa al'umma a cikin kunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel