Gwamnan APC A Babbar Jihar Arewa Ya Kori Kwamishina Da Wasu Mukarrabansa Guda 2

Gwamnan APC A Babbar Jihar Arewa Ya Kori Kwamishina Da Wasu Mukarrabansa Guda 2

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya kori kwamishinan noma Mista David Apeh tare da wasu jami’an gwamnatin guda biyu
  • Sakatariyar gwamnatin jihar Misis Folashade Ayoade-Arike ce ta sanar da korar mutanen uku nan take
  • Mutane biyun sune mai bai wa gwamna shawara kan ba da agajin gaggawa, Danladi Isah-Yunusa, da Hajiya Maryam Salifu shugabar hukumar kula da otal-otal da yawon bude ido ta jihar Kogi

Lokoja – Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, ya sanar da korar kwamishinan noma, Mista David Apeh.

Haka nan kuma ya kori mataimaki na musamman kan harkokin agajin gaggawa, Mista Danladi Isah-Yunusa, da Hajiya Maryam Salifu, shugabar hukumar kula da otel da harkokin yawon buɗe ido ta jihar Kogi.

Yahaya Bello ya kori kwamishinan noma na jihar Kogi
Gwamna Yahaya Bello ya kori kwamishinan noma na jihar Kogi tare da wasu mutane 2. Hoto: @OfficialGYBKogi
Asali: Twitter

Dalilin da ya sa gwamnan Kogi ya kori mutanen uku

Kara karanta wannan

Rusau a Kano: APC Ta Maida Raddi Ga Gwamna Abba Gida-Gida, Ta Roke Shi Alfarma 1

Korar mutanen uku dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar, Misis Folashade Ayoade-Arike, ta fitar a Lokoja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ko da yake ba a bayar da dalilin korar Apeh ba, Ayoade-Arike ta ce gwamnan ya amince da dakatar da kwamishinan nan take.

Sai dai ta ce an sallami Isah-Yunusa da Maryam Salifu daga muƙamansu ne saboda dalilai na karya ƙa'idojin aiki.

Hakan dai na zuwa ne a ƙasa da watanni shida da suka rage a gudanar da zaɓen gwamna a jihar ta Kogi.

Yadda na sha da ƙyar a harin da 'yan bindiga suka kai mun, ɗan takarar gwamnan SDP

A wani rahoto da jaridar The Punch ta fitar a kwanakin baya, ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin jam’iyyar SDP, a zaɓen 11 ga watan Nuwamba mai zuwa, Murtala Ajaka, ya yi ƙarin haske kan yadda ya tsallake rijiya da baya a lokacin da aka yi yunƙurin kashe shi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Ci Gaba Da Aikin Rusau Bayan Zazzafan Musayar Yawu Da Aka Yi Tsakanin Ganduje Da Kwankwaso

Lamarin, a cewarsa, ya faru ne a garin Koton Karfe, a kan hanyarsa ta dawowa daga fadar ɗaya daga cikin sarakunan gargajiya, inda ya je don bayyana masa burinsa na tsayawa takara.

Ajaka ya shaida wa manema labarai cewa, wani babban ɗan siyasa ne ya kitsa farmakin, inda yake zargin cewa shi ne ma ya bude ma ayarin motocinsa wuta.

Ya bayyana cewa kimanin mutane bakwai ne suka jikkata waɗanda aka kwantar a wani asibiti da bai bayyana ba.

Mai buƙata ta musamman ya zama Kakakin majalisar jihar Adamawa

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta yadda wani ɗan majalisa, mai buƙata ta musamman, Honarabul Bathiya Wesley, ya zama kakakin majalisar jihar Adamawa.

Wesley ya yi nasarar lashen zaɓen kakakin majalisar ne bayan neman goyon bayan masu ruwa da tsaki a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel