Majalisa Ta 8: Dan Majalisa Mai Bukata Ta Musamman Ya Zama Kakakin Majalisar Jiha A Arewa

Majalisa Ta 8: Dan Majalisa Mai Bukata Ta Musamman Ya Zama Kakakin Majalisar Jiha A Arewa

  • A karon farko, majalisar jihar Adamawa ta zabi mai bukata ta musamman Honarabul Bathiya Wesley don jagorantar majalisar ta 8
  • Honarabul Bathiya ya nemi takarar kujerar majalisar duk da yanayin halittar da Allah ya masa, ya ce shi ba ya daukar kansa a matsayin bukata ta musamman
  • A karshe ya godewa gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri bisa damar da ya ba shi ba tare da kawo cikas a zaben majalisar ba

Jihar Adamawa - Wani dan majalisa mai bukata ta musamman, Honarabul Bathiya Wesley ya yi nasarar zama kakakin majalisar jihar ta 8.

Bathiya wanda na daga cikin masu bukata ta musamman, ya yi nasara a zaben bayan ya nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki da kuma 'yan majalisar jihar.

Bathiya Wesley mai bukata ta musamman ya zama kakakin jihar Adamawa
Dan Majalisa, Bathiya Wesley. Hoto: TV360/.
Asali: Facebook

A wata tattaunawa da Daily Trust, Bathiya wanda ke wakiltar mazabar Hong ya ce bai taba daukar kansa a matsayin mai bukata ta musamman ba.

Kara karanta wannan

Ni ba barawo bane: Sanatan APC ya sharbi kuka a majalisa, ya fadi sharrin da aka masa

Dan majalisar ya ba da shawara ga masu bukata ta musamman

Ya kara da cewa wadanda ke daukar kansu haka, za su tabbata a haka ba tare da kawo ci gaba a kasa ba, cewar Daily Post.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan majalisar ya godewa gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri yadda ya ba da dama aka yi zabe ba tare da wani cikas ba.

Ya yi alkawarin yin aiki tare da 'yan majalisar don kawo ci gaba a cikin jihar baki daya.

Ya ce zai yi mulki wanda zai kunshi duk wani dan majalisa ba tare da nuna wariya ba

Ya kara da cewa zai bude kofa ga duk wanda ke son ci gaban jihar, kuma ba zai taba nuna wariya a shugabancinsa ba.

Inda ya ce duk wani abu da ya shafi shugabancin majalisar ba za a bar kowa a baya ba.

Kara karanta wannan

Yadda Hadin-kan da Majalisa ta ba Shugaba Buhari Ya Haifawa Najeriya Matsala - Sanata

Fintiri Ya Nemi Afuwa Game da Ciwon Zuciyan da Aka Sanyawa 'Yan Jihar

A wani labarin, Gwamna Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya nemi afuwan 'yan jihar bisa abubuwan da suka faru.

Baturen zabe ya bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zabe gwamnan jihar bayan ya doke Aishatu Binani.

Gwamnan a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa ya na sane da irin kuncin da 'yan jihar suka shiga a yayin tattara sakamakon zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel