Bola Tinubu Da Emefiele: Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Dakatar Da Gwamnan CBN

Bola Tinubu Da Emefiele: Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Dakatar Da Gwamnan CBN

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da dakatar da Godwin Emefiele, gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, sati 2 bayan fara mulkinsa.

Sai dai akwai wasu manyan abubuwan da ya kamata ku sani game da dakatarwar da aka yi wa tsohon gwamnan na CBN, waɗanda suka haɗa da batun sauya fasalin naira, bincike da ake a ofishinsa, da kuma halaccin dakatarwar da aka yi masa.

Dakatar da Emefiele da Shugaba Tinubu ya yi, ta yi wa ‘yan Najeriya da dama daɗi, waɗanda da yawa suka nuna hakan a shafukan sada zumunta da kuma majalisun zaman mutane a garuruwa.

Dalilan da suka sa aka dakatar da Emefiele
Wasu abubuwan da ya kamata a sani dangane da dakatarwar da Tinubu ya yi wa Emefiele. Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Babban dalilin da ya sa mutane suka yi farin ciki da dakatar da Emefiele da aka yi, shi ne saboda irin wahalhalun da tsarin sauya fasalin kuɗi ya janyo wa 'yan Najeriya, wanda kuma Emefiele ne ya zo da shi.

Emefiele ya kawo tsarin sauya fasalin kuɗin ne watanni 2 gabanin babban zaɓen 2023, wanda wasu ke ganin hakan na da alaƙa da siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Emefiele kuma ya cije akan tsarin da yazo da shi, duk kuwa da irin matsin tattalin arziƙin da al’ummar ƙasar suka shiga a lokacin. Ga abubuwa guda huɗu da ya kamata ku sani dangane da dakatarwar ta Emefiele:

1. Gdowin Emefiele ya sa 'yan Najeriya siyan kuɗi da kuɗi

Bayan bullo da tsarin sauya fasalin kudi da Emefiele ya yi, kuɗin Najeriya sun yi ƙaranci a hannun al'umma, wanda haka ya tilastawa mutane biyan maƙudan kuɗaɗe kafin su iya samun yawan kuɗin da suke buƙata.

Wasu masu sana'ar cirar kuɗi ta POS da suka zanta da Legit.ng, sun bayyana cewa suna biyan maƙudan kuɗaɗe wajen samun kuɗaɗe daga hannun ‘yan kasuwa, wanda hakan dole ya ja suka ƙara cajin da suke yi.

Yekini Shakirat wata da ta zanta da majiyar Legit.ng ta ce ta biya Naira 25,000 domin ta samu N250,000 don ta ci gaba da tafiyar da kasuwancinta.

Omobolanle, wata mai sana'ar POS, ta ce tana biyan N10,000 kafin a ba ta N100,000 don ta gudanar da sana’arta.

2. 'Yan Najeriya sun gaza sarrafa kuɗaɗensu

A lokacin tsarin sauya fasalin, yawancin 'yan Najeriya sun sha wahala wajen sarrafa kuɗaɗensu. Ba iya kuɗaɗe na takarda ba, har waɗanda ke cikin asusun ajiyar banki sun riƙa bayar da matsala kafin mutum ya cire su.

Wata dattijuwa da Legit.ng ta zanta da ita game da lamarin, ta koka da cewa:

“Na gaji haka nan. Dole na fara roƙon mutane kan su taimaka min na ajiye N7000 da na samu tun safe a asusun bankinsu, ban sani ba ko zan iya cirewa in zan je kasuwa ranar Litinin, saboda sun ce na’urorin cirar kuɗaɗe (ATM), ba sa ba da kuɗin.”

3. Ana gudanar da bincike a ofishin Godwin Emefiele

Bayan dakatarwar, an samu rahoto kan cewa jami’an tsaro na farin kaya (DSS), sun kama tsohon gwamnan na CBN.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, wata majiya a hukumar DSS ta bayyana cewa:

“Eh, ku sa ran (kama shi) zai faru. Ya kamata ace an daɗe da kama shi amma gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Buhari ta ba shi kariya. Yana da tambayoyi da yawa da zai amsa.”
"Saboda haka, ba za a bar shi ya fita ko kuma ya fece daga ƙasar ba. Don haka muna nemansa.”

4. Ta yi wu dakatarwar ta Emefiele ba ta cika sharuddan doka ba

Kamar yadda sashe na 11 na dokar CBN ta shekarar 2007 ya nuna, shugaban ƙasa yana da ikon ya soke naɗin gwamnan CBN, amma sai kashi biyu bisa uku (2/3), na ‘yan majalisa sun mara masa baya.

Wani ɓangare na sashen yana cewa:

"Shugaban ƙasa zai iya cire gwamnan CBN matuƙar dai kashi biyu bisa uku na majalisar dattawa za su goyi bayan tsige gwamnan da kan bukatar tsige shin."

Tinubu ya sanar da dakatar da Emefiele

Legit.ng ta kawo muku rahotan cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da yammacin ranar Juma'a.

Dakatarwar dai na zuwa ne bayan da gwamnatin ta Tinubu ta bayyana cewa akwai bincike da ake gudanarwa a ofishin gwamnan babban bankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel