"Tinubu Kadai Ba Zai Iya Cire Shi Ba": Lauyan Ya Yi Magana Kan Dakatar Da Emefiele

"Tinubu Kadai Ba Zai Iya Cire Shi Ba": Lauyan Ya Yi Magana Kan Dakatar Da Emefiele

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni
  • Wani lauyan Najeriya ya ce shugaban kasar bai da hurumin tsige Emefiele daga kan kujerarsa shi kadai
  • Sai dai, ya ce doka ta ba shi damar ladabtar da shi ciki harda dakatar da shi zuwa lokacin da za a kammala bincike

Lagos - Festus Ogun, wani lauya masanin kundin tsarin mulki ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai da ikon cire gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, shi kadai.

Ogun ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga dakatar da Emefiele da shugaban kasar ya yi a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni.

Shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnan CBN, Godwin Emefiele
"Tinubu Kadai Ba Zai Iya Cire Shi Ba": Lauyan Ya Yi Magana Kan Dakatar Da Emefiele Hoto: @officialABAT and @cenbank
Asali: Twitter

Sai dai kuma, lauyan ya yi bayani a wata wallafa da ya yi a Twitter cewar shugaban kasar na da wasu hukunce-hukunce na ladabtarwa da zai iya dauka kan gwamnan na CBN, wanda ciki harda dakatarwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: DSS Ta Kama Gwamnan CBN Godwin Emefiele Bayan Tinubu Ya Dakatar Da Shi

Ogun ya rubuta a Twitter:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Tinubu bai da ikon cire Emefiele shi kadai. Sai dai kuma, wata babbar kotun tarayya ta riki cewa yayin da shugaban kasa ba zai iya cire gwamnan CBN ba, yana iya daukar wasu matakan ladabtarwa kansa wanda ciki harda dakatar da shi. Kan dakatarwa kuwa, Emefiele na da hakkin a biya shi."

Tinubu ya dakatar da Emefiele don a binciki ofishinsa

Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele daga kujerarsa a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni, kuma ya fara aiki nan take domin bayar da damar ci gaba da kammala binciken da ake yi kan ayyukansa a matsayin gwamnan babban bankin kasar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan labarai na ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey ya fitar a yau Juma'a, 9 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Da Dumi Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan CBN, Emefiele

Rahotanni da ke zuwa sun nuna cewa jami'an hukumar tsaro na farin kaya wato DSS sun kama dakataccen gwamnan na CBN.

Da na hadu da Kwankwaso a fadar Villa, da ina iya dauke shi da mari, Ganduje

A gefe guda, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa idan da ya hadu da Rabiu Musa Kwankwaso, a fadar shugaban kasa da ke Abuja da ya mare shi.

Da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawa da Tinubu kan lamarin tsaro a jihar Kano bayan aikin rusau da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Ganduje ya nuna rashin gamsuwa da lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel