“PDP Da APC Basa Son Yan Najeriya”: Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa Labour Party

“PDP Da APC Basa Son Yan Najeriya”: Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa Labour Party

  • Tsohon dan takarar gwamnan PDP, Barista Ken Imansuangbon, ya yi murabus daga jam'iyyar inda ya koma Labour Party a jihar Edo
  • Imansuangbon ya samu kyakkyawar tarba daga tawagar shugaban LP na kasa, Julius Abure
  • Ya ce ya bar PDP ne saboda daga jam'iyyar lema har ta APC mai mulki duk kanwar ja ce

Jihar Edo - Cike da farin ciki, tsohon dan takarar gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Barista Ken Imansuangbon, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar Labour Party (LP) a jihar Edo.

Jaridar Independent ta rahoto cewa Imansugbon ya samu tarba daga bangaren shugaban jam'iyyar Labour Party na kasa a ranar Juma'a. 9 ga watan Yuni.

Yan siyasa a jihar Edo
“PDP Da APC Basa Son Yan Najeriya”: Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa Labour Party Hoto: Chidi W Wilfred
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Imansuangbon ya yi murabus daga matsayin dan PDP a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban PDP a jihar da shugaban gudunmarsa, karamar hukumar Esan ta kudu maso gabas a ranar Talata, 6 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Zaben 2024: Ɗan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka Daga Jam'iyyar PDP Zuwa LP

Duk kanwar ja ce daga APC har PDP

Da yake bayanin dalilinsa na komawa Labour Party, ya ce PDP da jam'iyyar All Progressive Congress (APC) basu damu da ci gaban yan Najeriya ba sai aljihunsu. Tsohon jigon na PDP ya bayyana jam'iyyun a matsayin iri guda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Imansuangbon ya ce:

"Ina son mika godiya ga Labour Party kan wannan damar da kuma sabonta muradin yan Najeriya. Tarihin siyasata na sananne ne. Na gudu PDP ba tare da na san cewa wuta na jefa kaina ba, PDP da APC duk kanwar ja ce, ba sa son yan Najeriya sai aljihunsu.
"Ya kuma zama dole na yi godiya ga matasan Najeriya wadanda suka marawa Labour Party baya kan abun da na kasa gani a tattare da tafiyar Obidient da Datti. A yau, mun san wanene shugaban kasa kuma yana a zukatan yan Najeriya. Duniya na kallon kotuna da kallon abun da za su yi. Wannan jam'iyya ce ta mutanen Najeriya, dalinai da masu rauni sosai."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Rushe Shugabanninta Na Gudanarwa a Jihohin Ebonyi Da Ekiti

Tinubu ya dakatar da Emefiele daga kujerar gwamnan CBN

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan labarai na ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey ya fitar a yau Juma'a, 9 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel