Gwamnan Kwara Ya Rage Wa Ma'aikata Ranakun Aiki Saboda Tsadar Fetur

Gwamnan Kwara Ya Rage Wa Ma'aikata Ranakun Aiki Saboda Tsadar Fetur

  • Gwamna Abdulrazak na jihar Kwara ya rage wa ma'aikata ranakun aiki daga kwanaki 5 zuwa 3 a kowane mako
  • Ya ɗauki wannan matakin na wucin gadi domin sauƙaƙa musu wahalhalun da aka shiga bayan tashin farashin man fetur
  • Shugabar ma'aikatan jihar Kwara, Misis Susan Modupe Oluwole, ce ta faɗi haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin

Kwara - Gwamnatin jihar Kwara karkashin jagorancin gwamna AbdulRahman AbdulRazak, ta amince da ɗaukar wasu matakai domin saukaƙa wa ma'aikata biyo bayan tashin farashin man fetur.

Channels tv ta rahoto cewa gwamna AbdulRazak ya amince da matakin rage ranakun aiki daga 5 zuwa 3 a kowane mako don sauƙaƙa wa mutane a wannan yanayi.

Gwamna Abdulrazak.
Gwamnan Kwara Ya Rage Wa Ma'aikata Ranakun Aiki Saboda Tsadar Fetur Hoto: channelstv
Asali: UGC

Shugabar ma'aikatan jihar Kwara, Misis Susan Modupe Oluwole, ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin 5 ga watan Yuni, 2023.

Sanarwan wacce ta fito ta hannun Sakataren watsa labarai, Murtala Atoyebi, ta ce mai girma gwamna ya umarci a rage wa kowane ma'aikaci ranakun aiki daga 5 zuwa 3 a kowane mako.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A sanarwan, shugabar ma'aikatan ta umarci ma'aikatu, sashi-sashi da hukumomin gwamnatin jihar su tsara jadawalin ranakun da kowane ma'aikaci zai riƙa zuwa aiki.

A cewarta, gwamna ya ɗauki wannan matakin ne domin saukaƙa wa mutane wahalhalun da aka shiga biyo bayan matakin FG na cire tallafin man fetur, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Haka zalika, Misis Oluwole, ta kara da jan hankalin ma'aikata su guji cin mutuncin alfarmar da mai girma gwamna ya musu duba da halin da aka wayi gari bayan cire tallafin man fetur.

Ta ce ofishinta zai ƙara matsa kaimi wajen kokarin sa ido kan abinda ke wakana a ma'aikatu domin tabbatar da ma'aikata na gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Wike, Umahi da Akpabio a Villa

A wani labarin na daban Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga taro yanzu haka tare da tsoffin gwamnoni uku a fadarsa ta Abuja.

Tsoffin gwamnonin da suka shiga ganawa da Tinubu sun haɗa da tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, David Umahi, da Godswill Akpabio.

Asali: Legit.ng

Online view pixel