“Gwamnati Mai Ci A Yanzu Ta Wucin Gadi Ce, Zan Karbo Kujerata a Kotu”, Atiku Abubakar

“Gwamnati Mai Ci A Yanzu Ta Wucin Gadi Ce, Zan Karbo Kujerata a Kotu”, Atiku Abubakar

  • Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwuiwar cewa zai amshi kujerarsa a kotu
  • Atiku ya bayyana hakan ne a wani taro na zaɓaɓɓun 'yan majalisu da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Bauchi
  • Ya kuma yi kira ga zaɓaɓɓun 'yan majalisun na PDP da su yi adawa tuƙuru, kada su yarda su zama 'yan amshin shata a majalisar

Bauchi - Dan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwuiwarsa kan cewa zai karɓi kujerarsa da yake zargin an amshe masa a kotu.

Atiku ya kira gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu a matsayin 'gwamnati ta wucin gadi', kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi ga zaɓaɓɓun yan majalisun PDP, a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Bauchi a ranar Asabar.

Atiku ya ce zai karbo kujerarsa hannun Tinubu
Atiku ya ce gwamnatin Tinubu ta wucin gadi ce, zai karbi kujerarsa a Kotu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku ya buƙaci 'yan majalisar PDP su jajirce da adawa

Atiku ya buƙaci ‘yan majalisun dokokin na jam’iyyar PDP na ƙasa, da kada su zama ‘yan amshin shata a majalisar wakilai ta ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa aikinsu a majalisar shi ne su zama 'yan adawa na gidi ga wannan 'gwamnatin ta wucin gadi'.

Atiku ya kuma ce a yanzu ba 'yan majalisun PDP ba ne ke da rinjaye a majalisa kamar yadda sakamakon zaɓe ya nuna, duk da akwai shari'o'i a gaban kotu, yana kira a garesu su jajirce da adawa kafin ya karɓo kujerarsa.

A cewarsa:

“Bisa ga sakamakon da hukumar zaɓe, INEC, ta bayyana da kuma jiran kammala shari'o'in zaɓe da ake a kotu, mambobinmu da aka zaɓa ba su ne mafi rinjaye a majalisar dokokin ƙasar ba.”
“A saboda haka, a halin yanzu, dole ne su shirya yin aiki a matsayin jajirtattun 'yan adawa, tare da yin shirin riƙe manya muƙamai a matsayin mafiya rinjaye idan aka kammala shari'o'in.”

Atiku ya ce kada 'yan majalisun PDP su zama 'yan amshin shata

Atiku ya kuma yi kira ga 'yan majalisun su dage tuƙuru wajen yin ayyuka domin cika alƙawuran da suka ɗaukarwa mutane a yayin yaƙin neman zaɓe.

Sannan ya ce dole ne su dage sosai wajen ɗora 'gwamnatin wucin gadin' a kan hanya domin yi wa 'yan ƙasa abin da ya kamata. Ya ce kada su yarda su zama 'yan amshin shata'.

A rahoton vanguard, Atikun ya kuma shawarci' yan majalisun da su riƙa gudanar da ayyukansu a tare ba a rarrabe ba. Sannan ya kuma jaddada musu cewa kada su mance da mutanen da suke wakilta.

Atiku ya soki Tinubu kan yadda ya cire tallafin man fetur

A wani labarin mai alaƙa da wannan, ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya soki shugaban ƙasa Bola Tinubu kan yadda ya cire tallafin man fetur.

Atiku duk da yana da kudurin cire tallafin shi ma, ya ce bai kamata Tinubu ya cire tallafin man fetur ɗin ba ba tare da ɗaukar wasu matakai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel