Bani da Shirin Sauya Sheka Daga PDP Zuwa Jam'iyar APC, Wike

Bani da Shirin Sauya Sheka Daga PDP Zuwa Jam'iyar APC, Wike

  • Tsohon gwamnan Ribas da ya gabata, Nyesom Wike, ya musanta jita-jitar cewa ya fara shirin sauya sheka zuwa APC mai mulki
  • Wike, jigon jam'iyyar PDP kuma jagoran tawagar G-5, ya ce sun gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ne don jaddada goyon baya
  • Ya ce a halin yanzu ba ya tunanin canja sheka daga PDP zuwa APC mai mulki kuma ba su yi magana mai kama da haka da Tinubu ba

FCT Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ribas da ya sauka ranar 29 ga watan Mayu, 2023, Nyesom Wike, ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ya fara shirin tattara kayansa ya koma APC.

Punch ta rahoto cewa Wike ya yi watsi da jita-jitar wacce ta yi ikirarin ya fara tunanin sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki bayan ganawa da shugaban kasa, Bola Tinubu.

Nyesom Wike.
Bani da Shirin Sauya Sheka Daga PDP Zuwa Jam'iyar APC, Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike, tare da gwamna Seyi Makinde na jiyar Oyo da tsohon gwamnan Delta, James Ibori, sun gana da Tinubu a fadar shugaban kasa ranar Jumu'a, 2 ga watan Yuni, 2023.

The Nation ta ce Manyan jiga-jigan babbar jam'iyyar adawa PDP sun ce sun ziyarci shugaba Tinubu ne domin tabbatar masa da goyon bayansu kwanaki huɗu bayan ya hau kujerar shugaban Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shin dagaske Wike zai koma APC?

Mista Wike ya musanta rahoton da ke cewa yana shirin sauya sheka zuwa APC kuma ya ƙaryata cewa hakan na ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka tattauna da Tinubu.

Yayin da manema labarai na gidan gwamnati suka tambaye shi ko batun ficewa daga PDP zuwa APC na cikin Ajendojin da suka tattauna da Tinubu, Wike ya ce:

"A'a, a'a bani da wannan tunanin, babu shirin sauya sheƙa a gabana. Mu 'yan Najeriya ne kuma mun zo ne mu ƙara tabbatar da goyon bayanmu ga shugaban ƙasa."
"Wannan kaɗai ake bukata a halin yanzu, don haka babu wani abu bayan shi."

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Fara Rusau a Birnin Kano

A wani labarin na daban kuma Gwamnan Kano ya fara rushe gine-ginen da aka yi a filayen da gwamnatin Ganduje ta cefanar.

Tun a wurin rantsuwar kama aiki, Abba Gida-Gida ya umarci hukumomin tsaro su kwace iko da wuraren da aka cefanar ba kan ƙa'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel