An Hangi Wike, Makinde, Ibori A Aso Rock, Sunyi Muhimmin Taro Da Shugaba Tinubu

An Hangi Wike, Makinde, Ibori A Aso Rock, Sunyi Muhimmin Taro Da Shugaba Tinubu

  • An rahoto cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi muhimmin taro da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP uku a Aso Rock
  • Wadannan jiga-jigan na jam'iyyar PDP sune Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, tsohon gwamnan Rivers Nyesom Wike da tsohon gwamnan Delta, James Ibori
  • An hangi mutanen uku a cikin Aso Rock Villa misalin wasu yan mintuna bayan karfe 4 na ranar Juma'a 2 ga watan Yuni

FCT, Aso Villa - An hangi Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da tsaffin gwamnonin Rivers da Delta, Nyesom Wike da James Ibori a fadar shugaban kasa na Aso Rock, Abuja, domin yin muhimmin taro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Tinubu ya gana da Wike da Makinde da Ibori a Villa.
Shugaba Tinubu na cigaba da yin muhimman taruka bayan rantsar da shi. Hoto: @officialABAT/Twitter, Seyi Makinde/Facebook and Nyesom Wike/Facebook
Asali: UGC

Kamar yadda The Nation ta rahoto, an hangi mutanen uku suna shiga fadar shugaban kasar misalin karfe 4.25 na yamma bayan shugaban Access Holding Plc, Herbert Wigwe, ya fito daga ofishin shugaban kasan.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 Game da Ministan Buhari da Tinubu Ya Zaba a Matsayin Sakataren Gwamnati

Makinde da Wike mambobi ne na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, wadanda suka taka muhimmin rawa wurin nasarar Shugaba Tinubu yayin zaben shugaban kasa, Tribune ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaba Tinubu ya yi nasara da tazara mai yawa a jihohin Rivers da Oyo, a cewar sakamakon da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta fitar.

A jihar Oyo, Tinubu ya samu kuri'u 449,884 domin kayar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar wanda ya samu kuri'u 182,977, don zama na biyu, shi kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour ya zo na uku da kuri'u 99,110.

Sai dai, a Jihar Rivers, Shugaba Tinubu ya samu kuri'u 231,591 daga kananan hukumomi 23 a jihar inda ya kayar da abokan hamayarsa na LP da PDP.

APC ta lashe zabe a kananan hukumomi 14, Jam'iyyar Labour kuma biyar, sai PDP ta lashe hudu a cewar sanarwar da Baturen Zabe, Farfesa Charles Adias ya bada.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago

Tinubu ya ce gwamnoni za su taimakawa gwamnatinsa samun nasara

A wani rahoton, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnoni suna da matukar muhimmanci a gwamnatinsa domin samun nasara.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 1 ga watan Yuni yayin wata ganawa da ya yi da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulrahman Abdulrazak da Seyi Makinde gwamnan jihar Oyo don taya shi murna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel