“Ka Cancanta”: FKK Ya Taya Gbajabiamila Murna Kan Zargin Nada Shi a Matsayin Shugaban Ma’aikatan Tinubu

“Ka Cancanta”: FKK Ya Taya Gbajabiamila Murna Kan Zargin Nada Shi a Matsayin Shugaban Ma’aikatan Tinubu

  • Femi Fani-Kayode ya taya Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai mai barin gado, murna kan zargin nada shi a matsayin shugaban ma'aikatan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Ba a tabbatar da nadin ba a hukumance, kuma shugaban ma'aikatan Gbajabiamila ya karyata rahoton a matsayin labarin kanzon kurege
  • Duk da rashin sanarwa da ke tabbatar da hakan a hukumance, ana ta yada labarin a soshiyal midiya kuma Fani-Kayode ya yarda cewa Gbajabiamila ya cancanci mukamin

Abuja - Babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Femi Fani-Kayode, ya taya Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar dattawa ta tara murna kan zargin nada shi a matsayin shugaban ma'aikatan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Koda dai ba a fitar da wata sanarwa a hukumance don tabbatar da hakan ba, rahoton ya yi zargin cewa ana ta rade-radin nadin a soshiyal midiya.

Fani Kayode da Femi Gbajabiamila
“Ka Cancanta”: FKK Ya Taya Gbajabiamila Murna Kan Zargin Nada Shi a Matsayin Shugaban Ma’aikatan Tinubu Hoto: Femi Fani-Kayode, Femi Gbajabiamila
Asali: Facebook

Legit.ng ta kuma rahoto a baya cewa shugaban ma'aikatan Gbajabiamila, Olanrewaju Smart Wasiu, ya yi watsi da rahoton nadin inda ya bayyana shi a matsayin kanzon kurege.

Fani-Kayode ya ce Gbabiamila ya cancanci mukamin shugaban ma'aikata

A halin da ake ciki, Fani-Kayode ya yi martani ga zargin nadin a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa Gbajabiamila ya cancanci mukamin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Ina taya abokina kuma dan uwana na fiye da shekaru 40, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila murna kan wannan nadi mafi cancanta a matsayin shugaban ma'aikatan jagoranmu, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu (@officialABAT).
"Wannan nadi ya tabbatar wa duniya cewa a wannan zamani kuma a karkashin wannan gwamnati ana nada mukamai ne bisa cancanta, biyayya da gogewa.”

A cewarsa, Gbajabiamila jajirtaccen mutum ne mai tsayawa tsayin daka a kan abu, inda ya ce yana da yakinin dan majalisar zai yi aiki mai kyau a sabon mukaminsa a matsayin shugaban ma'aikata. Ya kuma yi masa fatan alkhairi a wannan sabon mukami nasa.

Wike, Ganduje, Ribadu da wasu da ka iya shiga majalisar Tinubu

A wani labarin na daban, mun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu na shirin aiki da gogaggun yan siyasa a matsayin yan majalisarsa.

Ana ganin baya ga mambobin APC, sabon shugaban kasar na iya aiki da wasu yan jam'iyyun adawa da za su iya taimaka masa wajen cimma ajandarsa na daidaita tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel