Wasu Muhimman Bukatu Da Kungiyar Dattawan Arewa Ta Mika Zuwa Ga Shugaba Tinubu

Wasu Muhimman Bukatu Da Kungiyar Dattawan Arewa Ta Mika Zuwa Ga Shugaba Tinubu

  • Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cika alƙawuran yaƙin neman zaɓe da ya ɗauka kan tsaro da yaƙi da talauci
  • NEF ta kuma tunatar da Tinubu alƙawarin da ya yi na ba da fifiko kan matsalar tsaro, talauci, da ingantaccen shugabanci
  • Kungiyar ta ƙuduri aniyar yin aiki tare da Shugaba Tinubu da gwamnoni don tabbatar da cewa sun cikawa ‘yan Nijeriya alƙawuran da suka ɗauka

Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya cika alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zaɓe, kan maganar na tsaro da kawar da fatara.

Ƙungiyar ta ce Tinubu ya yi wasu muhimman alƙawura ga ‘yan Najeriya, wanda kuma take fatan cewa zai mutunta su, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin Da Buhari Ya Gaza Yi A Shekarunsa 8 Kan Mulki, Mataimakin Shugaban APC Ya Yi Bayani

Dattawan Arewa sun nemi Tinubu ya cika alkawuran da ya dauka
Kungiyar dattawan Arewa ta nemi Tinubu ya cika alkawuran da ya dauka na tsaro. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ƙungiyar ta tunatar da Tinubu kan rantsuwar da ya yi

Ƙungiyar, a cikin wata sanarwar ta taya murna ga shugaban ƙasa Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, ta tunatar da su irin rantsuwar da suka yi, wacce ya kamata ta zamto jagora a garesu har zuwa ƙarshen mulkinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran ƙungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ta ce:

“Kungiyar tana tunatar da Tinubu kan alƙawarin da ya ɗauka na bada muhimmanci kan matsalar tsaro, talauci da ingantaccen shugabanci, kuma ta yaba masa bisa tunaninsa na sake farfaɗo da martabar Najeriya da za ta bayyana a jikin talakawan ƙasar.
“Haka nan kuma yana da kyau a ba da fifiko kan batutuwa irinsu gwamnatin haɗaka, tabbatar da adalci da yaki da cin hanci da rashawa.
"Ya kuma kamata a kaucewa tsarukan da ka iya ƙara yawan talauci, kuma a duk sanda ake bukatar yanke hukunci mai tsauri, to ya kasance a yi sa cikin tausasawa, sanin ya kamata da kuma wayar da kan jama'a.”

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wakilan Amurka, Birtaniya Da Saudiyya, Ya Yi Wani Muhimmin Alkawari

Ƙungiyar za ta yi aiki tare da shugabanni

A rahoton jaridar Leadership, kungiyar ta kuma ƙara da cewa za ta yi aiki tare da sabbin shugabannin wajen ganin an cimma duka wasu ƙudurori da ake son aiwatarwa.

"Kungiyar za ta yi aiki tare da Shugaba Tinubu da gwamnoni domin tabbatar da cika alƙawuran da suka yi ga 'yan Najeriya na tsaro da kuma inganta tattalin arziki don rage talauci da fargaba."

Abinda Buhari ya gaza yi cikin shekaru takwas na mulkinsa

A wani labari da muka wallafa a baya, mun kawo muku wasu abubuwa da shugaba Buhari ya gaza aiwatarwa a tsawon wa'adin mulkinsa da ya kwashe shekaru takwas yana yi.

Mataimakin shugaban APC na ƙasa shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman Muhammed ne ya bayyana abubuwan da Buhari ya gaza aiwatarwa, ranar Laraba a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel