Kotu Ta Dage Sauraran Karar Peter Obi Saboda Rashin Lafiyar Lauyoyinsa 2

Kotu Ta Dage Sauraran Karar Peter Obi Saboda Rashin Lafiyar Lauyoyinsa 2

  • Kotun da ke sauraran korafe-korafen zaben shugaban kasa ta dage sauraran karar da Peter Obi ya shigar
  • Kotun ta dage karar ne zuwa gobe saboda rashin lafiyar lauyoyin Peter Obi guda biyu wadanda sune kan gaba
  • Lauyan Peter Obi, Awa Kalu shi ya nemi wannan alfarma a gaban kotun bayan sanar da babban lauyan Shugaba Tinubu

Abuja – Kotun sauraran korafe-korafen zabe na shugaban kasa ta dage sauraran karar da Peter Obi ya shigar saboda rashin lafiyar wasu daga cikin lauyoyisa guda biyu.

Vanguard ta tattaro cewa Peter Obi ya sanar da rashin lafiyar ma’aikatan nasa ne ta bakin lauyansa, Farfesa Awa Kalu a ranar Laraba 31 ga watan Mayu.

Peter Obi a Kotu
Kotu Ta Dage Sauraran Karar Peter Obi Saboda Rashin Lafiyar Lauyoyinsa, Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Lauyan ya kara da cewa rashin lafiyar mutanen biyu wadanda suka kasance jiga-jigai daga cikin lauyoyin Peter Obi, ya jawo cikas wurin kawo shaidu masu karfi da za su tabbatar da cewa zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a jam’iyyar APC akwai kura-kurai kuma an tafka magudi.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Rage Alawus Din Yan Bautar Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

Lauyan Peter Obi ya fadi matsalarsu

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ya mai shari’a, a tsarin mu na yau don ci gaba da wannan kara shi ne fara gabatar da shaidu, amma hakan ya samu tasgaro saboda wasu matsaloli da bamu yi tsammani ba.
“Wannan matsala ta shafi rashin lafiyar wasu daga cikin manyan lauyoyinmu, saboda haka ina neman alfarmar a dage zaman sauraran karar zuwa gobe."

Ya kara da cewa:

“Mun nemi wannan alfarma cikin kan-kan da kai da kuma neman afuwa.
“Ya mai shari’a ina tabbatar maka da cewa gobe zamu dawo nan da safe don ci gaba da karfin jiki.”

Lauyan Peter Obi ya ce ya fadawa kwamiti mai dauke da mutum biyar na Mai Shari’a Haruna Tsammani kafin a fara zaman cewa ya sanar da babban lauyan Shugaba Tinubu, Cif Olanipekun Wole akan abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Matakalar Taron Rantsar da Abba Gida Gida Ta Rushe Yayin Bikin Rantsar da Shi a Kano

Lauyan Shugaba Tinubu ya mika wuya

A martaninsa, lauyan Shugaba Tinubu, Chief Olanipekun ya fada wa kotun cewar ba ya jayayya da wannan neman alfarmar daga sauraran karar zuwa gobe, cewar Daily Post.

Peter Obi Zai Shafe Makonni Da Dama Yana Gabatar da Shaidu a Gaban Kotu

A wani labarin, kotun sauraran korafe-korafen zabe ta umarci Peter Obi, dan takarar jam'iyyar Labour ya gabatar da dukkan shaidunsa cikin makwanni uku.

Peter Obi da wasu 'yan takara suna kalubalantar zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a zaben da aka gudanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel