Bikin Rantsar Da Tinubu: Shehu Sani Ya Yi Hasashen Abinda Zai Faru Da Emefiele Bayan Saukar Buhari

Bikin Rantsar Da Tinubu: Shehu Sani Ya Yi Hasashen Abinda Zai Faru Da Emefiele Bayan Saukar Buhari

  • Tsohon sanata, Shehu Sani ya yi hasashen cewa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele, zai iya shiga tsaka mai wuya a gwamnatin Bola Tinubu
  • Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita, inda ya yi iƙirarin cewa rayuwar Emefiele a ƙarƙashin gwamnati mai jiran gado za ta kasance tamkar jakin dawa ne a hannun damisoshi
  • Wannan hasashe ya biyo bayan zargin da ake yi na cewa gwamnan na CBN ya yaƙi Tinubu a lokacin da yake neman shugabancin ƙasa

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi hasashen cewa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ba zai samu kyakykyawar alaƙa da gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Tinubu ba.

Shehu Sani a wani saƙo da ya wallafa wanda Legit.ng ta tsinkayo a shafinsa na Tuwita, ya ce rayuwar Emefiele a ƙarƙashin gwamnati mai jiran gado za ta kasance kamar jakin dawa ne a cikin garken damisoshi.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Ba Bola Tinubu Muhimmiyar Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Dab Da Rantsar Da Shi

Shehu Sani ya yi magana kan makomar Emefiele karkashin Tinubu
Sanata Shehu Sani ya ce Emefiele zai kasance kamar jakin dawa ne a hannun damisoshi a gwamnatin Tinubu.Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Shehu Sani, CBN
Asali: Facebook

Kamar yadda Legit.ng ta samu, Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita mako guda bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

A cewar Shehu Sani:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan Baba ya tafi, Emefiele zai zama kamar jakin dawa a hannun damisoshi.”

Ana zargin Emefiele da yaƙar Tinubu a lokacin zaɓen shugaban ƙasa

A lokacin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2023, an yi ta raɗe-raɗin cewa gwamnan babban bankin ya yaƙi takarar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

An zargi Emefiele da bullo da tsarin sauya fasalin Naira da kuma tsarin dakatar da zagayawar kuɗaɗe a hannun jama'a domin yi wa Tinubu zagon ƙasa a takararsa.

Emefiele zai fuskanci mummunan ƙalubale

Da hakan ne ake hasashen cewa gwamnan na CBN na iya fuskantar mawuyacin hali idan aka rantsar da Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Canja Fasalin Naira: An Faɗi Matakan da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka Kan Gwamnan CBN da Wasu Jiga-Jigai

'Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakunansu kamar haka:

Dele Olawanle, @dolawanle, ya ce:

“Abu ne mai sauƙi, zai bai wa sabbin mazauna fadar Aso Rock cikakken bayani, daga nan sai su yanke shawarar yadda za su hukunta shi."

Mickey Minnie, @Ninasteve007, kuma ya ce:

"Ya kamata ya yi ƙaura. Ba a wani ji daɗinsa ba. Kuɗaɗen canji a hannun talakawan Najeriya sun fi tsada akan na shafaffu da mai!. A ina irin hakan ke faruwa?"

Kamar A. Ariyo, @TheKamarAriyo, ya ce:

“Da yiwuwar ya bar ƙasar ne kawai kafin ranar 29 ga wata, wato ya yi gudun hijira har sai ƙura ta lafa. Sai dai kuma, Asiwaju ai babban ɗan siyasa ne."

Malamin Addinin ya yi hasashe kan batun rantsar da Tinubu

Wani malamin addini ya ce ya hasaso cewa za a rantsar da Tinubu a ranar 29 ga wata duk da ƙalubale na shari'a da ke gaban kotu.

Fasto Primate Olabayo ya bayyana cewa, tun a can baya ya taɓa shaidawa Bola Tinubu cewa, Allah ya riga da ya nuna masa cewa lallai zai zama shugaban ƙasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel