“Yan Najeriya Sun Yi Zabe Da Kyau”: Buhari Ya Ce Tinubu Ne Dan Takara Mafi Cancanta

“Yan Najeriya Sun Yi Zabe Da Kyau”: Buhari Ya Ce Tinubu Ne Dan Takara Mafi Cancanta

  • Shugaba Muhammadu Buhari, a jawabinsa na ban kwana, ya yarda cewa yan Najeriya sun dauki matakin da ya dace na zabar Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa na gaba
  • Buhari ya taya Tinubu murnar cimma dadaddiyar mafarkinsa sannan ya yaba ma cancanta, adalci da jajircewarsa wajen ci gaban Najeriya
  • Shugaban kasar mai barin gado ya nuna karfin gwiwar cewa shugabancin Tinubu zai kai kasar zuwa tafarkin ci gaba

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yan Najeriya sun yi tunani mai kyau na zabar Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa na gaba, yana mai cewa shine mafi dacewa a cikin yan takarar shugaban kasar da suka kara a zaben 2023.

Buhari ya fadi haka ne a jawabin ban kwana da ya yi a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu wanda Legit.ng ta sanyawa ido.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: “Ba Zan Taba Kiran Tinubu Da Shugaban Kasata Ba”, Shahararren Malamin Addini Ya Magantu

Bola Tinubu da Muhammadu Buhari
“Yan Najeriya Sun Yi Zabe Da Kyau”: Buhari Ya Ce Tinubu Ne Dan Takara Mafi Cancanta Hoto: Leadership
Asali: UGC

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, za a rantsar daTinubu wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Mafarkinka na son zama shugaban kasa ya zama gaskiya, Buhari ga Tinubu

A jawabinsa, Shugaban kasa Buhari ya taya Tinubu murnar cimma mafarkinsa na son zama shugaban kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce kishin kasar zababben shugaban kasar, gogewa da adalcinsa zai kai kasar ga tafarkin ci gaba.

Ya ce:

"Ga dan uwana, aboki kuma abokin aikina a harkar siyasa tsawon shekaru goma da suka shige - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ina taya ka murnar cimma mafarkinka, wanda ya zama gaskiya saboda kishinka na son saka Najeriya cikin jerin manyan kasashe a duniya.
"Lallai ka yi aiki don wannan rana kuma Allah ya daukaka kokarinka.
"Bana shakka cewa kishinka, cocgewa, adalci wajen hulda da mutane, daidaito, biyayyarka ga kasar da kokarinka na ganin Najeriya ta daukaka a duniya zai fisshe ka, karkashin jagorancin Ubangiji yayin da kake jagorantar kasar zuwa matakin daukaka.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Buhari Ya Ba ‘Yan Najeriya Hakurin Wahalar Da Gwamnatinsa Ta Jefa Su

"Kai ne dan takara mafi cancanta a cikin daukacin wadanda suka yi takara kuma yan Najeriya sun yi zabi mai kyau."

Ba zan taba kiran Tinubu shugaban kasata ba, Tunde Bakare

A wani labari na daban, Fasto Tunde Bakare, ya bayyana cewa ba zai taba kiran zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da shugaban kasarsa ba.

Yayin wani taro a ranar Asabar, malamin addinin kuma dan siyasa ya yi zargin cewa an yi magudi a lokacin zaben na 2023, yana mai cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta lalata tsarin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel