Buhari Ya Ba ‘Yan Najeriya Hakurin Wahalar Da Gwamnatinsa Ta Jefa Su

Buhari Ya Ba ‘Yan Najeriya Hakurin Wahalar Da Gwamnatinsa Ta Jefa Su

  • A yau ne Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa na karshe a matsayin Shugaban Najeriya
  • Shugaban mai barin-gado ya ce sun yi bakin kokari a mulki wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan
  • Amma hakan ya jawo wasu sun sha wahala na wani ‘dan lokaci, Buhari ya nemi afuwar mutanensa

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya roki afuwar al’ummar Najeriya game da tasirin da tsare-tsarensa su ka haifar a kasar.

The Cable ta ce wannan ya na cikin jawabin ban kwanan da shugaban mai barin-gado ya yi.

Dama can fadar shugaban kasa ta bada sanarwar cewa Mai girma Muhammadu Buhari zai yi jawabi a safiyar ranar Lahadi.

Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari da mai dakinsa Hoto: @Buhari Sallau
Asali: Facebook

A bayanan da ya yi, shugaban na Najeriya ya hada da bada hakuri domin ba za a rasa tsare-tsarensa da suka yi wa al’umma ciwo ba.

Kara karanta wannan

Mukamai 3 da Ake Sauraron Sabon Shugaban Kasa Ya Nada da Zarar Ya Shiga Ofis

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan ne jawabin karshe da za a saurara daga bakin Buhari a matsayin shugaban kasa, bayan wa’adinsa na mulki ya karaso,

Buhari ya ke cewa ya dauki duk wani mataki da ya ke kan mulki ne saboda cigaban kasa.

"Ina mai bada hakuri" - Buhari

"A kokarin farfado da tattalin arziki, mun dauki wasu matakai masu wahala, wadanda mafi yawansu su ka haifar da ‘da mai ido.
Wasu daga cikin matakan nan sun jawo an sha wahala na kankanin lokaci kuma ina mai ba ‘Yan Najeriya hakuri a kan hakan."

- Muhammadu Buhari

A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi kokarin hada-kan al’umma tare da ganin kaya sun samu a tsawon shekaru takwas da aka yi.

An rahoto mai girma shugaban kasar ya na cewa dama tun farko ya zo ne ya gyara abubuwa ko da wasu ba za su yabawa aikinsa ba.

Kara karanta wannan

Shekaru 8 Na Shafe Ina Ceto Yara ’Yan Najeriya Daga Hannun ’Yan Bindiga, Inji Buhari

Shugaban ya ce gwamnati ta inganta rayuwar mutanen karkara, sannan an koyawa matasan da ke birnin yadda za su nemi na kansu.

Na dace da zama Minista

An ji labari Ibinabo Dokubo ta fito ta na cewa ta na ganin ya kamata Bola Ahmed Tinubu ya yi mata sakayya, ta zama Minista idan ya hau mulki.

Jagorar ta APC a Ribas ta ce akalla zai yi kyau a bari ta kawo sunan wanda za a ba kujerar Minista tun da Asiwaju ya ce gwamnatinsa ta matasa ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel