May 29: “Ba Zan Taba Kiran Tinubu Shugaban Kasata Ba” – Fasto Tunde Bakare

May 29: “Ba Zan Taba Kiran Tinubu Shugaban Kasata Ba” – Fasto Tunde Bakare

  • Shugaban cocin Citadel Global Community Church, Fasto Tunde Bakare ya magantu a kan sabuwar gwamnati mai kamawa
  • Bakare ya ce ba zai taba kiran shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu da shugaban kasarsa ba
  • A cewarsa an yi magudi sosai a babban zaben 2023 yana mai zargin hukumar INEC da bata tsarin zaben gaba daya

Babban faston Najeriya kuma shugaban cocin Citadel Global Community Church, Fasto Tunde Bakare, ya bayyana cewa ba zai taba kiran zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da shugaban kasarsa ba.

Yayin wani taro a ranar Asabar, malamin addinin kuma dan siyasa ya yi zargin cewa an yi magudi a lokacin zaben na 2023, yana mai cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta lalata tsarin zaben.

Zababben shugaban kasa Bola Tinubu
May 29: “Ba Zan Taba Kiran Tinubu Shugaban Kasata Ba” – Fasto Tunde Bakare Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Ya fadi hakan ne yayin amsa tambayoyi bayan gabatar da jawabinsa kan shirin da aka yi ta Zoom wanda kungiyar yan Najeriya mazauna waje ta PTB4Nigeria ta shirya.

Kara karanta wannan

Uhuru Kenyatta Ya Ba Tinubu Muhimman Shawarwari Gabannin Rantsar Da Shi

An fara taron ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Asabar, 28 ga watan Mayu, jaridar Leadership ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake jawabi a lokacin taron, ya ce zaben 2023 bai kai yadda za a yarda da shi ba.

Da aka tambaye shi ko zai yi farin ciki don aiki da sabuwar gwamnati a matsayin ministan harkokin waje, ya yi dariya sannan ya ce zai fadi abun da ya fada ma shugaban kasa mai barin gado Muhammadu Buhari a makon jiya.

Bakare ya ce ya fada ma Buhari cewa wasu lokutan yana kiransa da shugaban kasar Najeriya wasu lokutan kuma yana kiransa da “shugaban kasata”, rahoton Punch.

Ya ce:

“A ranar Laraba da ta gabata, na kasance a Glass House inda aka kange shi (Buhari) a yanzu saboda ana gyara a ainahin gidan. Na ce na yi maka haka. Ina so ka sani cewa, saboda abun da ke kewaye da zuwanka mulki a kan tafarkin gaskiya da rashin aikata rashawa, amma yanzu za ka mika mulki ga wani wanda bai da wannan darajar.”

Kara karanta wannan

May 29: Muhimman Abubuwa 4 Da Tinubu Zai Fara Yi Bayan Rantsar Da Shi

Ba zan taba kiran Asiwaju da shugaban kasata ba, Bakare

Ya bayyana cewa a wajen “kowani taro kafin a wanke wannan barnar, zan kira Asiwaju a matsayin shugaban kasar Najeriya amma ba zan taba kiransa da shugaban kasata ba.”

Ya ce ban yi zaben ba don haka babu wanda zai ce ya sha kaye a zaben.

Bakare wanda ya yi takara a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar 14 ga watan Yunin 2022 kuma bai samu kuri’a ko daya ba ya ce:

“Na yi takara a zaben fidda gwanin, kuma akwai daruruwan mutane da suka yi takara kawai ta hanyar janyewa, don haka babu abun kunya a abun da muka yi. Mun fada ma masu mulki gaskiya cikin mintuna bakwai.
“Bana nan da suka yi zabe, bana nan da suka bani sifili, amma mun samu wannan sifilin da tarin martaba.”

Dole a fada ma Buhari cewa ya gaza, Gwamna Ortom

Kara karanta wannan

Malami, Emefiele Da Wasu Yan Majalisar Buhari Da Za a Ji Su Shiru Da Zaran Tinubu Ya Karbi Mulki

A wani labari na daban, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya yi wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo.

Ortom ya ce Buhari ya gaza a matsayin shugaban kasa kuma dole a fada masa, cewa ba a taba lalatacciyar gwamnati irin wannan ba a tarihin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel