Majalisar Dattawa Ta Shuga Zaman Gaggawa Kwana 2 Gabanin Rantsar da Tinubu

Majalisar Dattawa Ta Shuga Zaman Gaggawa Kwana 2 Gabanin Rantsar da Tinubu

  • Mambobin majalisar dattawa sun fara tattaruwa a zauren majalisar tarayya da Abuja domin zaman gaggawa kan wasu kudirori
  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ne yake jagorantar zaman wanda za'a yi muhara kan muhimman kudirori
  • Wannam shi ne karo na biyu da majalisar dattawa ta 9 ta kira zaman gaggawa tun lokacin da ta fara aiki a 2015

Abuja - Kwana biyu kacal gabannin rantsar da zababben shugaban kasa, majalisar dattawan Najeriya ta kira zaman gaggawa a zaurenta da ke Abuja.

Channels tv ta rahoto cewa har kawo yanzu babu sahihin bayani kan muhimmin abinda majalisar dattawan zata tattauna a wannan zama yau Asabar, 27 ga watan Mayu, 2023.

Majalisar dattawa.
Majalisar Dattawa Ta Shuga Zaman Gaggawa Kwana 2 Gabanin Rantsar da Tinubu Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Zuwa yanzu dai an ga Sanatoci na zuwa ɗaya bayan ɗaya suka shiga zauren majalisar dattawan amma shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan, bai ƙariso ba.

Legit.ng Hausa ta gano cewa wannan shi ne karo na biyu da majalisar dattawa ta 9 wacce wa'adinta ke dab da karewa, ta kira zaman gaggawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Karo na farko da majalisar ta kira makamancin wannan zaman shi ne a lokacin Annobar Korona Birus domin ta amince da kuɗin yaƙar cutar da kokarin daƙile yaɗuwarta.

Kudirorin da majalisa zata yi muhara a kai sun bayyana

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kudirorin da suka jawo wannan zaman gaggawa kamar yadda takardar Oda ta majalisar ta nuna sun kunshi:

"Kudirin garambawul ga ƙarin kasafin kuɗin 2022 da sauran batutuwa masu alaƙa da shi, 2023 (SB. 1124), zaman karatu na biyu, wanda Sanata Gobir Ibrahim Abdullahi (Sokoto ta gabas) ya gabatar."
"Kudirin garambawul ga dokokin babban bankin Najeriya (CBN) C4 dokokin tarayyan Najeriya 004 da wasu batatuwa masu alaƙa 2023 (SB. 1125), shi ma zama na biyu."

Legit.ng Hausa ta gano cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya isa zauren kuma shi ke jagorantar zaman yanzu haka.

Gwamna Wike Ya Bukaci FG Ta Kara Yawan Kasafin da Take Ware Wa Yan Sanda

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙata yawan kuɗin da take ware wa rundunar 'yan sanda.

Gwamnan ya ce duk gwamnatin ba zata kare rayuwa da dukiyar talakawanta ba, ba ta da amfani kuma ba ta kama hanyar shugabanci nagari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel