29 Ga Watan Mayu: Cunkoso Da Wasu muhimman Abubuwa 4 Da Ya Kamata Mazauna Abuja Su Yi Tsammanin Gani

29 Ga Watan Mayu: Cunkoso Da Wasu muhimman Abubuwa 4 Da Ya Kamata Mazauna Abuja Su Yi Tsammanin Gani

  • Najeriya za ta sake kafa tarihi a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, lokacin da za a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16
  • Babban birnin tarayya za ta shirya babban taro da ba za a taba mantawa da shi ba a tarihi
  • A halin da ake ciki, wannan ci gaban zai shafi mazauna babban birnin tarayya ta bangare mai kyau da mara kyau

Abuja - Gabannin bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ake ta jira, za a gudanar da harkoki da dama a wannan rana da ma kafin ranar.

Mazauna babban birnin tarayya za su karbi bakuncin manyan masu fada aji na gida da waje wadanda za su halarci bikin rantsar da Tinubu.

Asiwaju Bola Tinubu
29 Ga Watan Mayu: Cunkoso Da Wasu muhimman Abubuwa 4 Da Ya Kamata Mazauna Abuja Su Yi Tsammanin Gani Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

A wannan zauren, za mu jero wasu muhimman abubuwa biyar da mazauna birnin tarayya za su iya gani a yayin bikin rantsar da Tinubu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Abba Gida-Gida Ya Gayyaci Sanusi Zuwa Bikin Rantsar Da Shi

1. Tsauraran matakan tsaro da yiwuwar rufe harkokin jama'a

Mazauna Abuja na iya fuskantar dokar hana zirga-zirga daga cikin matakan tsaro da za a shimfida a ranar rantsar da shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, za a karkatar da hanyoi, rufe su da saka shinge bincike masu tsauri a fadin hanyoyin da zai sada mutum da Eagle Square, inda za a rantsar da zababben shugaban kasar.

Wannan ci gaban zai kuma sanya wasu kasuwanci rufewa zuwa lokacin da za a kammala bikin rantsarwar.

2. Shigowar manyan baki na gida da waje

Shakka babu Tinubu mutum ne da ya shahara a nahiyar Afrika, kuma manyan mutane na gida da waje za su halarci bikin rantsar da shi a matsayin zababben shugaban kasa.

Mazauna birnin tarayya na iya ganin shigowar manyan yan siyasa, yan diflomasiyya da fitattun mutane na gida da waje.

Kara karanta wannan

Tinubu: Kashim Ya Fadawa ‘Yan Najeriya Gaskiyar Zancen Abin da Zai Faru a Mulkinsu

Tun a ranar Talata, 23 ga watan Mayu, ne tsohon firai ministan Birtaniya, Tony Blair ya iso Najeriya don wannan taro.

3. Cunkoson ababen hawa

Wannan abu ne da ba za a taba guje masa ba domin dai za a samu cunkoson ababen hawa a kuryar babban birnin tarayya saboda bikin rantsarwar.

Haka kuma za a rufe hanyoyi da kuma karkatar da hanyoyin da za su takaita zirga-zirgar motocin kasuwa a cikin babban birnin.

4. Habbakar tattalin arziki

Bikin rantsar da Bola Tinubu zai amfani harkokin kasuwanci sosai, kuma birnin Abuja zai samu habbaka wajen tattara kudaden shiga yayin bikin rantsarwar.

Jiragen sama, motocin haya da jiragen kasa, gidajen cin abinci da shagunan siyar da kayayyaki za su yi ciniki sosai.

Manyan mutane na gida da waje sune za su bayar da gudunmawa wajen bunkasa dukkanin wadannan tattalin arziki.

5. Hutu

Wannan shine abu mafi dadi da ake sanya ran zai faru a lokacin bikin rantsarwar. Abuja babban birni ne da ke cike da ma'aikatan gwamnati, ma'aikata masu zaman kansu, yan kasuwa da mazauna birnin wadanda za su ji dadin wannan dan gajeren hutu da za a bayar don su huta.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Daure Usman A Gidan Yari Kan Satar 'Bible' 4 Da Kudade

Tuni gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 29 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin yan Najeriya su huta da kallon yadda za a rantsar da shugaban kasarsu na 16 a talbijin.

Buhari ya zagaya da Tinubu fadar villa

A wani labarin, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zagaya da Bola Tinubu don nuna masa ciki da wajen fadar shugaban kasa.

Hakan ya kasance ne jim kadan bayan shugabannin sun idar da sallar Juma'a a fadar gwamnati a yau 26 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel