NYSC Ta Bayyana Gaskiya Kan Satifiket Din Dan Majalisar Jam'iyyar APC, Benjamin Kalu
- Hukumar masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta wanke Hon. Benjamin Kalu sannan ta tabbatar da cewa ya yi wa ƙasa hidima
- A cikin wata takardar tabbatarwa da babban darektan NYSC ya rattaɓawa hannu, an tabbatar da an ba Kalu satifiket ɗin kammala hidimtawa ƙasa
- Hon Kalu shine ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a kujerar mataimakin kakakin majalisar wakilai
FCT, Abuja - Hukumar masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta bayyana gaskiya kan taƙaddamar da ta biyo bayan satifiket ɗin Hon Benjamin Kalu, zaɓaɓɓen ɗan majalisa mai wakiltar Bende a jihar Abia a majalisar Wakilai.
Kalu, wanda shine zaɓin jam'iyyar APC a takarar kujerar mataimakin kakakin majalisar wakilai, ya samu satifiket ɗin tabbatarwa daga NYSC.

Asali: Facebook
Takardar tabbatarwar wacce Legit.ng ta samu a ranar Talata, 23 ga watan Mayu, akwai sanya hannun babban darektan hukumar NYSC, Ibrahim A Muhammad.
Takardar na cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ina son sanar da ku cewa Mr. Kalu Benjamin Okezie mai satifiket mai lamba A001773067, wanda ya ke da lambar kod na jiha EN/108/0567 ya kawo kansa NYSC ɗauke da satifiket ɗinsa na asali domin sake tabbatar da su a ranar 23 ga watan Mayun 2023.
"An tabbatar da satifiket ɗin inda aka gano cewa halastaccen satifiket ne wanda NYSC ta bayar."
Kalu Ya Janye Daga Takarar Kujerar Kakakin Majalisa
Benjamin Kalu wanda ya baya yana daga cikin masu neman kujerar kakakin majalisar wakilai ta 10, ya bayyana janyewarsa daga yin takarar shugabancin majalisar.
Kalu ya bayyana cewa ya janye daga takarar ne, bayan jam'iyyar APC ta cimma matsayar kai kujerar, yankin Arewa maso Yamma.
Abbas Da Kalu Sun Ziyarci Abdullahi Adamu
A wani rahoton na daban kuma, Abbas Tajudeen, zaɓin jam'iyyar APC a kujerar shugabancin majalisar wakiƙai, ya sanya labule da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu.
Abbas ya samu rakiyar abokin takararsa, Benjamin Kalu, da wasu zaɓaɓɓun ƴan majalisa na jam'iyyar APC,. A yayin taron na su, sun buƙaci jam'iyyar da ta shawo kan sauran ƴan takarar da ke adawa da su, su dawo su mara musu baya.
Asali: Legit.ng