Abbas Da Kalu Sun Ziyarci Shugabannin Jam'iyyar APC, Sun Bukaci Su Sanya Baki a Rikicin Majalisa Ta 10

Abbas Da Kalu Sun Ziyarci Shugabannin Jam'iyyar APC, Sun Bukaci Su Sanya Baki a Rikicin Majalisa Ta 10

  • Ɗan takarar kujerar shugabancin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya ziyarci shugaban jam'iyyar APC tare da mambobin NWC
  • Abbas ya ziyarci shugabannin jam'iyyar ne tare da abokin takararsa da kuma wasu zaɓaɓɓun ƴan majalisar wakilai
  • Ɗan takarar ya nemi uwar jam'iyyar ta ƙasa da ta sanya baki wajen shawo ƙan sauran ƴan takarar da ke neman kujerar su mara masa baya

Abuja - Ɗaya daga cikin masu takarar neman kujerar shugabancin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya buƙaci shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, da ya sanya baki kan rikicin shugabancin majalisa ta 10.

Abbas, wanda shine ɗan takarar da Bola Tinubu da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na APC ke goyon baya, ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci sakatariyar jam'iyyar APC ranar Talata a birnin tarayya Abuja, Premium Times ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da APC Ta Kalubalanci Zabaɓben Gwamnan PDP

Abbas da Kalu sun gana da Adamu Abdullahi
Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, da sauran mahalarta taron Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Abbas ya gana da mambobin kwamitin gudanarwar na ƙasa, tare da abokin takararsa, Benjamin Kalu, da mambobin tawagar Joint Task Group.

Abbas na son NWC su sanya baki a rikicin shugabancin majalisa

Da ya ke jawabinsa, Abbas ya bayyana cewa yakamata jam'iyyar ta yi magana da sauran ƴan takarar domin shawo kansu. Idan jam'iyyar ta yi hakan, shi kuma ya yi alƙawarin yin duk mai yiwuwa domin kare abinda jam'iyyar ta ke so."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Ina son na roƙe ku da ku ƙara wani abu a CV ɗin ku, wanda shine kawo shugabancin majalisa ta 10. Kun yi komai, ciki har da tabbatar da nasarar jam'iyya a zaɓen da ya wuce. Wannan ne kaɗai abinda ya rage mu ku da ku cimmawa."
"Kun yi yunƙurin farko. Yanzu abinda ya rage shine ku kira duk waɗanda za su yi zaɓe da su fito su zaɓi ƴan takarar ku."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Dau Zafi, Ta Dakatar Da Wasu Manyan Jiga-Jiganta a Jihar Kogi

"Mu na roƙon ku da ku kira sauran abokan takararmu. A shirye mu ke mu yi aiki tare domin ciyar da ƙasar nan gaba."

Gwamna Wike Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Sanata Akpabio

A wani rahoton kuma, kun ji cewa gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya nuna goyon bayansa ga takarar sanata Godswill Akpabio, ta kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10.

Gwamna Wike ya ce zai yi duk baƙin ƙoƙarin da zai iya yi domin ganin Akpabio ya samu nasarar ɗarewa kan shugabancin majalisar dattawan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel