Ondo 2024: Wanene Zai Lashe Zaben Fidda Gwanin Kujerar Gwamna a Jam’iyyar PDP?

Ondo 2024: Wanene Zai Lashe Zaben Fidda Gwanin Kujerar Gwamna a Jam’iyyar PDP?

Gabanin zaben gwamna da za a yi a jihar Ondo a ranar 16 ga watan Nuwamba, harkokin siyasa a jihar da ake yi wa take da 'hasken rana' na kara daukar zafi yayin da jam'iyyun siyasa suka fara gudanar da zaben fidda gwani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a baya ta sanar da cewa za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu a jihar daga ranar 6 zuwa 27 ga Afrilu, 2024.

Ondo: Lucky Aiyedatiwa ya lashe tikitin APC

Biyo bayan fitar da jadawalin INEC, jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da nata zaben a ranar 20 ga watan Afrilu, inda gwamna mai ci, Lucky Aiyedatiwa ya samu nasara.

Kara karanta wannan

Daga karshe Ganduje ya bayyana wadanda suka kitsa dakatar da shi daga jam'iyyar APC

Manyan 'yan takarar PDP a zaben fidda gwani na kujerar gwamnan Ondo
Ondo 2024: Jam’iyyar PDP za ta gudanar da zaben fidda gwani a ranar 25 ga Afrilu. Hoto: Sola Ebiseni, Otunba Bamidele Akingboye, Agboola Ajayi
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jam’iyyar APC ta fitar da sanarwa a shafin Twitter a safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Afrilu, Aiyedatiwa ya doke ‘yan takara 15 a zaben.

A halin da ake ciki kuma, masu neman takara daga jam’iyyar adawa ta PDP na ci gaba da yin 'yan dabarbaru domin samun tikitin takara a jam’iyyar.

PDP ta tantance 'yan takara 7 a Ondo

A karshen watan Maris ne jaridar Premium Times ta ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta tantance 'yan takarar gwamna bakwai da za su fafata a zaben fidda gwani.

‘Yan takarar sun hada da Adeolu Akinwumi, Olusola Ebiseni, Bamidele Akingboye, Kolade Akinjo, Bosun Arebuwa, John Mafo da Agboola Ajayi.

A cewar rahoton jaridar Vanguard, za a gudanar da zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP a ranar Alhamis, 25 ga Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi rashin babban jigo, tsohon gwamna ya kama gabansa

Ondo: Manyan 'yan takara 3 a PDP

Legit Hausa ta jero bayanin wasu fitattun ‘yan takara da ya kamata ku sani a yayin da jam’iyyar PDP ke shirin gudanar da nata zaben tsaida gwanin.

1. Agboola Ajayi

Agboola Ajayi dai ya kware a fagen siyasa, sanin doka da kasuwanci, inda ya taba rike mukamin mataimakin gwamnan jihar Ondo daga 2017 zuwa 2021, kamar yadda shafinsa na Wikipedia ya nuna.

Da yawa na ganin cewa kwarewar da yake da ita a sha'anin mulkin jihar zai iya bashi nasara kan abokan karawarasa.

Sai dai murabus din da yayi daga jam'iyyar APC na iya zama cikas gare shi, inda wasu ke kokonton sahihancin biyayyarsa ga shugabanni da mambobin jam'iyyar PDP.

Duk da cewa Ajayi ya mallaki dukkanin abubuwan da ake bukata, sai dai yana bukatar gamsar da jam'iyyar tare da fitar da tsari mai kyau na tsamo jihar Ondo daga halin da take ciki.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje karo na biyu: APC ta mayar da martani mai zafi ga 'yan tawaren jam'iyyar

2. Otunba Bamidele Akingboye (OBA)

Otunba Bamidele Akingboye (OBA) dan takara ne mai cike da kwarewa a harkar kasuwanci wanda kuma ya yi amanna da cewa siyasa na tafiya kafada-da-kafada da kasuwanci,

Burin da OBA ya sa a gabansa shi ne bunkasa jihar ta hanyar sarrafa ma'adanai da masana'antu da ta mallaka, tare da nemo masu zuba hannun jari a jihar, rahoton mujallar The Chronicle.

Sai dai kwarewar OBA a kasuwanci ba lallai ya ba shi tikitin PDP ba la'akari da cewa mulki na bukatar kwarewa ta ɓangarori da dama ba iya kasusuwanci ba.

3. Sola Ebiseni

Chief Sola Ebiseni ya taba riƙe muƙamin shugaban karamar hukumar Ilaje/Ese Odo, kuma ya yi kwamishina a lokuta da dama a jihar Ondo, kamar yadda jaridar The Guardian ta rahoto.

La'akari da hazakar da ya nuna a kujerar kwamishinan muhalli da kuma shugaban hukumar shari'a ta jihar na iya ba shi nasara a zaben fidda gwanin jam'iyyar na PDP.

Kara karanta wannan

Ondo: Jam'iyyar APC ta ayyana zaben fidda gwanin jihar 'Inconclusive', ta fadi dalilai

Sai dai kuma kamar kowanne dan Adam, Ebesina na da na shi matsalolin da wasu ke ganin kujerar gwamna ta yi masa nauyi, duk da kasancewarsa sakataren kungiyar Yarbawa.

Kammalawa

Ko ma dai me zai faru, mazauna jihar Ondo sun zura ido da kwadayin ganin ‘yan takarar da za su fito daga jam’iyyun APC, PDP da sauran jam’iyyun siyasa.

Wannan ne zai ba su damar yanke shawara mai inganci kan dan takara da jam’iyyar siyasar da za su kada wa kuri’a a ranar 16 ga Nuwamba, 2024.

Tsohon gwamnan Imo ya bar PDP

A wani labarin kuma, jam'iyyar PDP ta fuskanci matsala bayan da Hon Emeka Ihedioha, tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar.

Ihedioha wanda kuma tsohon gwamnan jihar Imo ne ya shafe shekaru 26 a cikin jam'iyyar PDP wacce a yanzu ya ce ta canja akala daga yadda ya santa a kai a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel