APC: Ana Tangal Tangal da Kujerarsa, Ganduje Ya Fadi Wadanda Za Su Iya Gyara Najeriya

APC: Ana Tangal Tangal da Kujerarsa, Ganduje Ya Fadi Wadanda Za Su Iya Gyara Najeriya

  • Duk da matsalar da shugaban APC kyae ciki, ya tabbatar da cewa jam'iyyarsu ita ce kadai hanyar dakile matsalolin kasar
  • Abdullahi Ganduje ya tabbatar da haka ne a yau Laraba 24 ga watan Afrilu a Gombe inda ya ce APC ce kadai mafita a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne yayin da Ganduje ke cikin matsala kan badakalar kudi a Kano da kuma tangal-tangal da kujerarsa ke yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya yi albishir ga 'yan Najeriya kan mulkin Bola Tinubu.

Abdullahi Ganduje ya ce jam'iyyar APC ita ce kadai za ta dakile matsalolin kasar a halin da ta ke ciki a sauki.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kaddamar da titin 'Abdullahi Ganduje' da aka gina a wajen Kano

Shugaban APC, Ganduje ya bayyana jam'iyyar a matsayin mafita ga 'yan ƙasar
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce jam'iyyar ce kadai mafita ga Najeriya. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Wane albashir Ganduje ya yi ga Najeriya?

Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka a Gombe yayin mika tutocin jam'iyyar ga 'yan takarar shugabancin kananan hukumomi a jihar, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya ce jam'iyyar karkashin mulkin Bola Tinubu ta himmatu wurin kawo karshen matsalolin kasar baki daya.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa Tinubu ya samar da yanayi mai kyau wanda zai taimaka wurin inganta rayuwar 'yan ƙasar baki daya, cewar Daily Post.

"Duba da kundin dokokin APC, jami'yyar ta cimma abubuwa da dama musamman a matakin kasa."
"Ku duba yadda APC ta kawo abubuwan ci gaba da more rayuwa a Gombe karkashin jagorancin Inuwa Yahaya."
"Wannan ya tabbatar da cewa APC ce kadai za ta kawo karshen matsalolin Najeriya gaba daya."

- Abdullahi Ganduje

Ganduje ya bukaci goyon bayan 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Daga karshe Ganduje ya bayyana wadanda suka kitsa dakatar da shi daga jam'iyyar APC

Ganduje ya roki 'yan Najeriya da su ci gaba da ba Shugaba Bola Tinubu goyon baya domin kawo karshen matsalolin kasar.

Ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya kan bin tsarin Shugaba Bola Tinubu wurin ayyukan ci gaba da raya al'umma.

An rahoto ya kara da cewa APC ta na alfahari da jihar ganin irin abubuwan ci gaba da aka kawo a jihar inda ya ce ta na daga cikin jihohi mafi ci gaba a kasar.

An sake dakatar da Ganduje a Kano

A wani labarin, kun ji cewa wani tsagin jam'iyyar APC ya sake tabbatar da dakatar da Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar.

Tsagin jam'iyyar da ke gundumar Ganduje a jihar Kano ya yi fatali da matakin da wasu suka yi na musanta korar Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel