Dan Takarar Shugaban Kasa, Ya Bankado Hujjoji Da Za Sua Hana a Rantsar Da Bola Tinubu

Dan Takarar Shugaban Kasa, Ya Bankado Hujjoji Da Za Sua Hana a Rantsar Da Bola Tinubu

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Democratic Alternative Party, Victor Vishnay, ya yi kiran da aka soke rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu
  • Vishnay ya kuma yi kiran da a soke zaɓen shugaban ƙasa na 2023 sannan ya zargi shugaba Buhari da yin katsalandan kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasan na watan Fabrairu
  • Ɗan takarar shugaban ƙasar ya bayar da shawarar mataimakin shugaban ya amshi ragamar ƙasar nan ko a kafa wani kwamiti da zai kula da ƙasar bayan Buhari ya sauka a ranar 29 ga watan Mayu

Abuja - Victor Vishnay, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Democratic Alternative Party, ya yi kiran da a soke rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A wani rahoton jaridar Thisday, Vishnay ya yi zargin cewa hanyar zaɓen da aka bi ta samar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, cike ta ke da maguɗi da zamba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: "Ba Makawa Dole Na Zama Shugaban Kasa a Najeriya," Peter Obi

An bukaci shugaba Buhari ya soke rantsar da Tinubu
Victor Vishnay ya bayyana dalilan da yakamata su sanya a soke rantsar da Bola Tinubu Hoto: Femi Adesina, Yemi Osinbajo
Source: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa, ɗan takarar shugaban ƙasar, ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar, 13 ga watan Mayu a lokacin wata tattaunawa da manema labarai.

Ya bukaci shugaba Buhari ya soke zaɓen 2023

Vishnay ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da ya soke zaɓen 2023, saboda ingancinsa bai kai yadda ake so ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Ina kira ga dukkanin ƴan Najeriya da su yi kira ga shugaban ƙasa, ya soke babban zaɓen 2023, musamman zaɓen shugaban ƙasa saboda maguɗin da aka yi."
"Mu na buƙatar sauyi, sauyi na gaskiya, neman ganin mun samu ingantacciyar Najeriya zai fara ne daga soke zaɓen. Ba ayi gaskiya da adalci a zaɓen ba."

Vishnay ya bayyana cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai iya miƙa ragamar ƙasar nan ga mataimakinsa, ko ya kwafa wani kwamiti wanda zai kula da ƙasar bayan ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu - Yanzu: Mazauna Abuja Sun Maka Tinubu A Kotu Don Hana Rantsar Da Shi, Lauya Ya Yi Martani

"Hanya daya mafita kawai itace shugaban ƙasa ya soke zaɓen, ya bayar da dalilan soke zaɓen sannan ya sauka. Mataimakin shugaban ƙasar sai ya hau kan kujerar shugaban ƙasa, ko kuma ya kafa wani kwamiti, wanda zai kula da ƙasar nan bayan ya bar mulki." A cewarsa

Abbas da Kalu Sun Ziyarci Gwamnan Jihar Legas, Sun Nemi Goyon Bayansa

A wani labarin na daban kuma, ƴan takarar da jam'iyyar APC ke marawa baya a kujerar shugabancin majalisar wakilai, sun ziyarci gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu, sun je wajen gwamnan ne dai da ƙoƙon bararsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng