Yanzu: Mazauna Abuja Sun Maka Tinubu A Kotu Don Hana Rantsar Da Shi, Lauya Ya Yi Martani

Yanzu: Mazauna Abuja Sun Maka Tinubu A Kotu Don Hana Rantsar Da Shi, Lauya Ya Yi Martani

Wasu mutane 5 da suka kira kansu da 'yan Abuja masu rajistar katin zaɓe sun shigar da ƙara a gaban kotu, su na neman a dakatar da rantsar da Tinubu

  • Sun nemi kotun ta kuma haramtawa alƙalin alƙalai ko wani ma'aikacin shari'a, damar rantsar da Tinubu ba tare da an cika sharuɗan da suka zayyano ba
  • Sun ce dole ne sai mutum ya samu kaso 25 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a babban birnin tarayya sannan ya cancanci a rantsar da shi

FCT, Abuja - Wasu mutane 5 'yan asalin birnin tarayya Abuja sun ɓuƙaci kotu ta dakatar da rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da ake shirin yi cikin kwanaki 17 masu zuwa.

Masu shigar da ƙarar dai sun buƙaci a hana alƙalin alƙalai na ƙasar, mai shari'a Olukayode Ariwoola ko wani daga cikin masu iko daga rantsar da kowane ɗan takara ne da ya yi takarar shugabancin ƙasa a zaɓen da ya gabata na ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekara.

Kara karanta wannan

Fitaccen Gwamnan APC Ya Naɗa Sarakunan Gargajiya Sati 2 Kafin Ya Bar Ofis

Bola Tinubu
Bola Tinubu. Hoto: This Day
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rahoton Vanguard, mutanen sun kuma bayyana cewa mazauna birnin na tarayya na da 'yancin sanin cewa ko wanda za'a rantsar ya cika sharaɗin samun aƙalla kaso 25 na ƙuri'un da aka kaɗa a birnin tarayya Abuja.

Sun dogara da dokar da ta ke cewa babu wani mutum da za a iya rantsarwa a matsayin shugaban ƙasar Najeriya ba tare da ya samu kaso 25 na ƙuri'un da aka kaɗa a birnin tarayya Abuja.

Ba za a sanar da mutum ya lashe zaɓe ba in bashi da kaso 25

Dokar ta sashe na 134(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya wacce ta ke cewa ba ma za a sanar da cewa wani ɗan takara ya lashe zaɓe ba har sai ya samu aƙalla kaso 25 na ƙuri'un da aka kaɗa a yankin birnin na tarayya.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Jigon Jam'iyyar APC Ya Bayyana Abu 1 Da Ka Iya Kawo Cikas Ga Rantsar Da Tinubu

Haka nan doƙar ta ƙara da cewa ba za a rantsar da mutum ba har sai ya cika wannan sharaɗi na samun kaso 25 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a Abuja.

Haka nan kuma dokar ta jaddada cewa babu wani ɗan takara da za a rantsar a matsayin kwamandan askarawan Najeriya har sai ya kasance ya na da kaso 25 cikin 100 na ƙuri'un Abuja.

Shugaban ƙasa mai ci zai ci gaba da riƙe ƙasa

Baya ga haka masu ƙarar sun dogara da sashe na 135(1) da ke cewa muddun ba a samu wani daga cikin 'yan takara da ya cika sharuɗan da doka ta tanada na a rantsar da shi ba, to shugaban ƙasar da ke kai zai ci gaba da riƙe ƙasar.

Sannan kuma sun dogara da dokar da ke cewa babu bayar da satifiket ko kuma gudanar da rantsuwar sabon shugaba har sai dai idan doka ta tabbatar da cewa ya cika duka sharuɗan da aka gindaya.

Kara karanta wannan

Zaɓen Shugaban Kasa: Atiku Ya Ɗauki Manyan Lauyoyi 19 Don Kwace Nasara Daga Hannun Tinubu A Kotu, Jerin Sunaye

Sunayen mutanen da suka shigar da ƙarar waɗanda kuma suka kira kansu a matsayin 'yan Abuja masu rajistar katin zaɓe sune: Anyaegbunam Okoye, David Adzer, Jeffery Ucheh, Osang Paul da Chibuike Nwachukwu.

Mutanen dai sun ambaci sunan ministan shari'a na ƙasa da kuma sunan alƙalin alƙalai a cikin takardar ƙarar.

Jaridar Leadership ta ce mutanen biyar sun shigar da ƙarar neman dakatar da rantsar da Tinubu ne a babbar kotun birnin tarayya da ke Abuja.

An zargi Tinubu da Wike da ƙulla wata maƙarƙashiya

A wani labari da muka wallafa a baya, kun ji cewa an zargi Tinubu da Wike da ƙullawa Atiku wata maƙarƙashiya dangane da shari'arsa da Bola Tinubu.

Wata ƙungiyar rajin bin doka da oda ce dai ta yi wannan zargin, in da ta ce Tinubu ya bai wa Wike kwangilar tarwatsa hujjojin da Atiku ya dogara da su a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng