Daga Sanata Zuwa Uwargidan Shugaban Kasa: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Oluremi Tinubu
Nan da wasu ƴan kwanaki kaɗan, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai yi bankwana da shugabancin ƙasar nan, sannan ya miƙa ragamar mulkin ƙasar nan a hannun zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Bikin rantsar da Bola Tinubu zai gudana ne a ranar 29 ga watan Mayu, wanda hakan zai zo da sabon sauyi ga lamuran siyasar Najeriya.
Ba kamar sauran gwamnatocin da suka shuɗe ba tun daga shekarar 1999, gwamnatin Tinubu za ta zo ne cike da iyalansa waɗanda sun goge sosai a siyasa.

Source: Twitter
Wannan iyalan na Tinubu za su sanya ƴan Najeriya, su ga uwargidan shugaban ƙasa ta daban, saɓanin waɗanda suka saba gani a baya.
Wannan uwargidan shugaban ƙasar, ba kowa ba ce face Oluremi Tinubu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan
Tun Yanzu: Kashim Shettima Ta Faɗi Kuskuren da Shugaba Buhari Ya Tafka a Mulkinsa Kamar Na Jonathan
Legit.ng ta tattaro abubuwa biyar da yakamata ku sani dangane da ita:
1. Ta yi sanata sau uku
Uwargidan shugaban ƙasa mai jiran gado, Oluremi Tinubu, ta wakilci Legas ta tsakiya, a majalisar dattawan Najeriya, har sau uku.
Zamanta sanata har sau uku, na nuna cewa uwargidan shugaban ƙasar mai jira gado za ta fahimci siyasa sosai, fiye da sauran takwarorinta da suka gabace ta, tun daga shekarar 1999.
2. Ta Kafa gidauniyar New Era
Remi, kamar yadda aka fi kiran ta da shi, ta yi suna bayan ta kafa gidauniyar New Era, wata gidauniya mai kula da cigaban mata da ƙananan yara.
3. Sau biyu tana zama uwargidan gwamnan jihar Legas
Oluremi itace uwargidan gwamnan jihar Legas tun daga shekarar 1999 har zuwa 2007, lokacin da mijinta ya ke a kujerar gwamnan Legas.
Lokacin da ta ke uwargidan gwamnan Legas, ta kawo shirye-shirye masu yawa domin amfanin mata, ciki har da gidauniyar New Era.
4. Babbar fasto ce a RCCG

Kara karanta wannan
"Shirin Komawa Daura": Buhari da Aisha Sun Ɗau Harama, Sun Koma Gidan Shugaba Mai Barin Gado
Wani abin sani dangane da uwargidan shugaban ƙasan mai jiran gado shine, babbar fasto ce a cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG).
Abin sha'awa shine duk da banbancin addini da ke tsakaninta da mijinta, Bola Tinubu, sun zauna lafiya a rayuwar auren su.
5. Remi za ta koma cikakkiyar matar aure daga ranar 29 ga watan Mayu
Cikin raha lokacin da ya ke jawabinsa na samun nasara a zaɓe, Bola Tinubu, ya yi nuni da cewa matarsa ba za ta koma majalisar dattawa ba. Sai dai za ta zama cikakkiyar matar aure.
Betara Ya Bayyana Dalilinsu Na Bijirewa Matsayar APC Kan Shugabancin Majalisa Ta 10
A wani labarin na daban kuma, mai neman kujerar kakakin majalisar wakilai ta 10, ya bayyana dalilin su na bijirewa matsayar jam'iyyar APC kan shugabancin majalisar.
Mukktar Aliyi Betara, ya bayyana cewa ba za su amince da matsayar jam'iyyar ba, saboda ba a shawarce su ba.
Asali: Legit.ng