Majalisa Ta 10: Tinubu Ba Zai Maimaika Kuskuren da Buhari da Jonathan Ba, Shettima

Majalisa Ta 10: Tinubu Ba Zai Maimaika Kuskuren da Buhari da Jonathan Ba, Shettima

  • Mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, Kashim Shettima, ya ce Tinubu ba zai maimaita kurkuren Buhari da Jonathan ba
  • Ya ce kiri-kiri majalisar wakilan tarayya ta hana Buhari cimma abubuwa da yawa a zangon mulkin farko
  • Wannan dai na zuwa ne bayan jam'iyyar APC ta sanar da Abbas da Kalu a matsayin yan takarar da take goyon baya

Abuja - Gwamnatin zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da ke dab da kama aiki na kokarin kaucewa abinda ya faru a majalisar wakilan tarayya a 2011 da 2015, inji Kashim Shettima.

Premium Times ta rahoto zababɓen mataimakin shugaban ƙasan na cewa Tinubu ba zai maimaita kurkuren da ya faru ba lokacin da majalisar wakilai ta koma yaƙar jam'iyya mai mulki.

Kashim Shettima.
Majalisa Ta 10: Tinubu Ba Zai Maimaika Kuskuren da Buhari da Jonathan Ba, Shettima Hoto: Kashim Shettima/facebook
Asali: Facebook

Ya ce tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jonathan, ga rasa shawo kan gwamnatinsa tun da aka wayi gari Aminu Waziri Tambuwal, ya zama kakakin majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu

Shettima ya ƙara da cewa wannan kuskuren kaɗai ya taimaka wajen shan kayen jam'iyyar PDP a babban zaɓen 2015.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane kuskure Buhari ya yi a mulkinsa?

Haka zalika ya ce shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, bai taɓuka abun a zo a gani ba a zangon mulkinsa na farko saboda rashin tsoma baki a zaben shugabannin majalisa.

Sanata Shettima ya yi wannan bayani ne a wurin ganawarsa da Tajudeen Abbas, Ben Kalu da wasu mambobin, "Join Task," gamayyar zababbun yan majalisa da suka yi alƙawarin goyon bayan duk wanda APC ta nuna.

Rahoton jaridar ya tattaro cewa jam'iyyar APC mai mulki ta ɗauki Abbas da Kalu a matsayin 'yan takarar da take goyon baya a matsayin kakaki da mataimakin kakakin majalisar wakilai bi da bi.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalili 1 Rak da Yasa Tinubu da APC Suka Zabi Akpabio da Abbas, Shettima Ya Tona Gaskiya

Wannan mataki ya gamu da babban tasgaro, inda wasu 'yan takara suka yi fatali da wanda APC ta tsayar.

Daga nan suka haɗa kai suka kafa tawagar da suka raɗa wa suna, "Coalition of Progressive Speakership Aspirants (COPSA)" domin yaƙar Abbas, wanda ya samu goyon bayan jam'iyya.

Dalilin da Yasa Muka Zabi Akpabio a Abbas a Matsayin Shugabannin Majalisa, Shettima

A wani labarin kuma Kashim Shettima Ya Bayyana Babban Abinda Ya Sa Suka Zabi Yan Takara A Majalisar Tarayya Ta 10

Zababben mataimakin shugaban kasan ya ce jam'iyyar APC ta ɗauki Akpabio ne domin gudun kar mutum 4 na farko a Najeriya su zaman mabiya addini ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel