Shirye-shiryen Miƙa Mulki: Aisha Buhari Da Remi Tinubu Sun Zaga Fadar Shugaban Kasa

Shirye-shiryen Miƙa Mulki: Aisha Buhari Da Remi Tinubu Sun Zaga Fadar Shugaban Kasa

  • Aisha Buhari da Sanata Oluremi Tinubu sun zagaya gidan gwamnati don nuna ma matar shugaban mai jiran gado ciki da wajen fadar
  • Tuni iyalan shugaba mai barin gado suka fara shirye-shiryen barin fadar domin baiwa iyalan zaɓaɓɓen shugaban damar shigowa
  • Remi Tinubu ta yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta yi abubuwan da za su amfani 'yan Najeriya baki ɗaya

Abuja - Uwargidan shugaban ƙasa mai barin gado, Aisha Buhari ta ta zagaya wasu muhimman wurare tare da mai ɗakin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mai jiran gado, Sanata Oluremi Tinubu.

Sun dai gudanar da wannan zagaye ne a ranar Talatar nan, in da Aisha ta nunawa Remi wasu muhimman guraren da iyalan shugaban ƙasa ke zama a cikin gidan gwamnatin kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Mai Jiran Gado, Bola Tinubu Zai Ƙara Tafiya Ƙasar Waje? Gaskiya Ta Bayyana

Aisha da Remi Tinubu
Aisha Buhari da Remi Tinubu. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ta nuna mata in da za su zauna in an rantsar da su

A yayin da suke zagayen, Aisha ta nunawa matar Tinubun gidan gilashi da ta ce gida ne da shuwagabannin ƙasa ke zama a lokacin barin karagar mulki tare da miƙa shi zuwa wata gwamnatin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba a dai baiwa 'yan jaridar damar ɗaukar hotuna a wasu ɓangarori na gidan ba a lokacin zagayen.

Ta ƙara da cewar gurin da ya fi kowane tsaro shine in da aka tanadar a matsayin makwanci ga shugaban ƙasar ta Najeriya da kuma iyalansa su kaɗai.

Aisha ta ce gidan gilashin an yi shi ne domin shugaban ƙasa da ke barin gado saboda a samu damar yin gyare-gyare a ainihin babban gidan.

Oluremi Tinubu ta nuna godiyarta

Da take nata jawabin, matar Tinubu ta nuna matuƙar godiyarta bisa irin tarbar da Aisha Buhari ta yi ma ta. Haka nan kuma ta sha alwashin yin iya bakin ƙoƙarin ta wajen yin abubuwan da za su amfani 'yan Najeriya kamar dai yadda PM News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Majalisa ta 10: Kakaba Shugabannin Majalisar Wakilai Ya Kawo Rudani a APC, Wasu 'Yan Takara Sun Yi Bore

Shugaba Muhammadu Buhari dai zai miƙa ragamar mulkin ƙasar hannun Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, bayan shafe zagaye biyu ya na gudanar da mulki.

Ganin likita ya hana Buhari dawowa daga Landan

A labarin da muka wallafa a baya, an bayyana cewa shugaba Buhari ya tsawaita wa'adin tafiyarsa da ya yi zuwa Birtaniya domin ya tsaya ya ga likita.

Hadimin shugaban mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ne ya shaidawa manema labarai hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel