Majalisa ta 10: Kakaba Shugabannin Majalisar Wakilai Ya Kawo Rudani a APC

Majalisa ta 10: Kakaba Shugabannin Majalisar Wakilai Ya Kawo Rudani a APC

  • Da alamu sabuwar rigima na neman ɓarkewa kan shugabancin majalisar wakilai ta 10
  • Wata ƙungiya ta yi Allah wadai da zaɓin Tajudeen da Kalu a matsayin waɗanda za su shugabanci majalisar
  • Rahotanni na yawo kan cewa jam'iyyar APC za ta miƙa ragamar shugabancin majalisar a hannun mutanen biyu

Abuja - Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna, Democrats Alliance for Good Governance (DAGG), ta yi Allah wadai da rahotannin da ke yawo na zaɓar Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu a matsayin wadanda za su shugabanci majalisar wakilai.

Ana raɗe-raɗen cewa APC ta zaɓi Abbas Tajudeen wanda ya fito daga jihar Kaduna, a matsayin kakakin majalisar, ya yin da Benjamin Kalu wanda ya fito daga jihar Abia, a matsayin mataikamin sa.

Zabar Tajudeen da Kalu shugabannin majalisar Wakilai ya kawo rudani
Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Haka kuma wasu daga cikin zaɓaɓɓun ƴan majalisar sun nuna ɓacin ran su kan zaɓar mutanen biyu da aka yi a asirce a birnin tarayya Abuja, ranar Juma'a, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Bayan Kwashe Kwanaki a Hannun 'Yan Sanda, An Bayar Da Belin Yunusa-Ari, An Gindaya Masa Sharudda

kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Dr. Williams Martins, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, a Abuja ya bayyana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun shiga ɓacin rai da jin an ci amanar mu, musamman da mu ka ji cewa ɗan takarar da ake son an kai shi domin gabatar da shi ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa."
"Hakan a gare mu ba wai kawai ƙasƙanci bane, face cin fuskanci ga ƙimar ƴan Najeriya da miliyoyi suka fito suka kaɗa mu su ƙuri'un su, a zaɓen ranar 25 da na ranar zaɓen cike gurbi."

Kodinetan ya kuma yi gargaɗi kan yin wani abu da zai iya kawo rashin jituwa da haɗin kai a majalisar wakilai ta 10, cewar rahoton Vanguard.

Sai dai, ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun ƴan majalisar, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya yi watsi da raɗe-raɗen cewa suna jin zafin Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: An Samu Wata 'Yar Majalisa Mace Ta Fito Takarar Kujera Mai Gwabi a Majalisa

A kalamansa:

"A yayin da ba mu da matsala da neman takarar sa, muna son sake nanata cewa abinda mutane su ke so shine zai tabbatar da wanda zai zaman kakakin majalisa na 10."

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Gwamnonin Arewa Na Goyon Bayan Bola Tinubu

A wani rahoton na daban kuma, shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa ya bayyan dalilin su na goyon bayan komawar mulki yankin Kudancin Najeriya.

Simon Lalong ya ce duk da sun goyi bayan Tinubu, da farko ba don shi bane suka haƙiƙance sai mulki ya koma yankin Kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel