Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP Ya Yi Magana Kan Nasarar Sa a Kotu, Ya Aike Da Wani Muhimmin Sako Ga APC

Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP Ya Yi Magana Kan Nasarar Sa a Kotu, Ya Aike Da Wani Muhimmin Sako Ga APC

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yaba da hukuncin kotun ƙoli wanda ya tabbatar da nasarar sa a zaɓen gwamnan jihar na watan Yulin shekarar 2022
  • Adeleke ya sadaukar da wannan nasarar da ya samu ga mutanen jihar Osun, inda ya yi nuni da cewa lokaci ya yi da za su kwashi romon dimokuraɗiyya
  • Gwamnan ya kuma nemi abokin hamayyar sa Gboyega Oyetola da jam'iyyar APC, da su zo a haɗa kai da su domin ciyar da jihar gaba

Osogbo, Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, ya yaba da hukuncin kotun ƙoli wanda ya tabbatar da nasarar sa a zaɓen gwamnan jihar na watan Yulin shekarar 2022.

Kotun ƙolin a ranar Talata, 8 ga watan Mayu, ta tabbatar da nasarar gwamnan akan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ɗan takarar ta, Gboyega Oyetola.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Taya Gwamnan PDP Murnar Nasara a Kotu, Ya Nemi Wata Alfarma 1

Gwamna Adeleke ya yi magana kan nasarar sa a kotu
Adeleke ya yi magana kan nasarar sa a kotun ƙoli Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

Da ya ke jawabi bayan hukuncin kotun, gwamna Adeleke, a shafin sa na Twitter, ya ce ya sadaukar da wannan nasarar ga ubangiji da mutanen jihar Osun, inda ya ƙara da cewa lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan shugabanci don samar wa da mutanen jihar romon dimokuraɗiyya.

Gwamnan ya kuma nemi abokin hamayyar ta sa, Gboyega Oyetola da jam'iyyar sa ta APC, da su marawa gwamnatinsa baya, inda ya ƙara da cewa lokaci ya yi da za a haɗa hannu da kowa domin cigaban jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani ɓangare na jawabin na sa na cewa:

"Wannan hukuncin zai ba mu damar mayar da hankali wajen kawo romon dimokuraɗiyya a jihar Osun. Lokaci ya yi da za mu haɗa hannu tare domin ciyar da jihar nan gaba."

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Kotun Koli Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Ci Zaben Gwamnan Osun

A Karon Farko Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Nasarar Da Gwamnan Adeleke Ya Samu a Kotu

Da zu mun kawo rahoto cewa, shugaba Buhari ya yi magana kan nasarar da gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya samu a kotun ƙoli, inda ta tabbatar da shi a matsayin sahihin gwamnan jihar.

Shugaba Buhari, ya yi kira ga mutanen jihar da su ba gwamnan haɗin kan da ya dace domin ganin ya ciyar da jihar su gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel