Sanata Akpabio Da Wasu Zababbun Sanatocin APC Sun Sanya Labule Da Tinubu

Sanata Akpabio Da Wasu Zababbun Sanatocin APC Sun Sanya Labule Da Tinubu

  • Wasu daga cikin zaɓaɓɓun sanatocin da aka zaɓa a jam'iyyar APC sun ziyarci Bola Tinubu
  • Sanatocin sun sanya labule da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ne bisa jagorancin sanata Akpabio
  • Sanata Akpabio shine wanda Bola Tinubu ya ke so ya shugabanci majalisar dattawa ta 10

Jihar Rivers - Zaɓaɓɓun sanatocin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), sun ziyarci zaɓaɓɓaen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ranar Alhamis.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa, sanatocin sun ziyarci Tinubu ne a birnin Port Harcourt, bayan ya kammala ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamna Wike ya gudanar a jihar.

Akpabio da wasu sanatocin APC sun kebe da Tinubu
Bola Tinubu da wasu jiga-jigan APC Hoto: Newsweeknigeria.com
Source: UGC

Daga cikin sanatocin da ke wajen taron sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, Shuaib Salisu daga jihar Ogun, Solomon Olamilekan daga jihar Legas, da wasu da dama.

Kara karanta wannan

Ba Sanya: Ana Dab Da Rantsar Da Shi, Bola Tinubu Ya Sha Wani Muhimmin Alwashi

A cikin wani bidiyo an nuna sanata Akpabio yana gabatar da zaɓaɓɓun sanatocin ga Bola Tinubu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya gaisa da zaɓaɓɓun sanatocin cikin raha a bidiyon.

Takarar neman kujerar shugabancin majalisar dattawa, ta janyo cece-kuce a tsakanin sanatocin da aka zaɓa a majalisar dattawa ta 10, a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

Manyan sanatoci guda shida da suka fito daga yankuna daban-daban na ƙasar nan, sun nuna aniyar su ta neman kujerar shugaban majalisar dattawan.

Wasu daga cikin masu neman kujerar bayan sanata Akpabio sun haɗa da Jibrin Barau (jihar Kano), Abdulaziz Yari (jihar Zamfara), Gwamna Dave Umahi (jihar Ebonyi), Orji Uzor Kalu (jihar Abia), Osita Izunaso (jihar Imo) da Sani Musa (jihar Niger)

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa manyan masu faɗa a ji a jam'iyyar sun cimma matsayar kai kujerar yankin Kudu maso Kudu, domin sanata Akpabio, cewar rahoton Daily Trust.

Jam'iyyar APC dai har yanzu ba ta sanar da yankin da za ta kai kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10 ba.

Kara karanta wannan

"Abu 1 Mu Ke Jira", Daga Karshe APC Ta Bayyana Dalilin Rashin Fitar Da Tsarin Shugabancin Majalisa Ta 10

An Bayyana Ainihin Dalilin Da Ya Sanya Osinbajo Ya Yi Takara Da Tinubu

A wani rahoton na daban kuma, dalilan da suka sanya Farfesa Yemi Osinbajo neman kujera ɗaya da Bola Tinubu sun bayyana.

Wani na kusa da Osinbajo, shine ya bayyana su, inda ya ce mataimakin shugaban ƙasar ya yi takarar ne domin cigaban al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng