Jigon Jam'iyyar APC Ya Garzaya Kotu Neman a Dawo Masa Da Kayayyakin Da Ya Raba Lokacin Zabe

Jigon Jam'iyyar APC Ya Garzaya Kotu Neman a Dawo Masa Da Kayayyakin Da Ya Raba Lokacin Zabe

  • Jigo a jam'iyyar APC a jihar Kebbi, ya gsrzaya kotu neman ta tilasta a dawo masa da kayayyakin da ya bayar a raba lokacin zaɓe
  • Jigon ya dai ba ƴaƴan jam'iyyar PDP kayayyakin domin su tattaro masa masu kefa ƙuri'a ranar zaɓe
  • Sai dai sun yi sama da faɗi da kayayyakin wanda hakan ya sanya shi zuwa gaban kotun neman haƙƙin sa

Jihar Kebbi - Wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ƙaramar hukumar Maiyama ta jihar Kebbi, Adamu Mai Lemu Andari, ya garzaya kotu yana neman a kwato masa kayayyakin da ya rabawa ƴan jam'iyyar PDP a lokacin zaɓen gwamna da na ƴan majalisar dokokin jihar.

Andari ya je kotun majistare ne mai zaman ta a Jega inda ya nemi ta kwato kayayyakin da ya rabawa wasu mutum biyu, Auwal Mai Hadisi Arosiya da Mai gari Gyamro Arosiya, domin su nemo masa masu kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓe.

Kara karanta wannan

"Ba Ka Bi Na Bashin Komai": Wasu Muhimman Abubuwa 5 Da Tinubu Ya Fada Yayin Da Wike Ya Gayyace Shi

Jigon APC ya nemi kotu ta sanya a dawo masa da kayan da ya raba lokacin zabe
Gangamin taron 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar Kebbi Hoto: Sunnews.com
Asali: UGC

Andari yana neman kotun ta sanya a dawo masa da buhuna 35 na taki, atamfa 70, buhunan shinkafa 2 da N50,000 da ya ba ƴaƴan jam'iyyar PDP su biyu, cewar rahoton Tribune.

Lauyan mai shigar da ƙara, Bashir Umar, ya ce mutum biyun da ake ƙara an kawo su gaban kotun ne saboda cin amana, yaudara da karkatar da abinda wanda yake karewa ya basu su raba zuwa amfanin kan su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar lauyan mai shigar da ƙarar:

"Mu na roƙon kotu da ta kwato mana kayayyakin sannan ta hukunta mutanen biyu bisa karya doka da aikata laifi."

Lauyan wanda ake ƙara, Haruna Ubandawaki, a yayin da yake martani kan jawabin lauyan mai shigar da ƙara, ya ce yana son kotun ta bayyana ko tana da hurumin sauraron ƙarar wacce ta faɗo a sashi na 121, sakin layi na 6 na dokar zaɓe.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Matashin Saurayi Ya Burma Wa Mahaifiyarsa Wuƙa Har Ta Mutu a Kano

Lauyan wanda ake ƙarar ya ce waɗanda ya ke karewa sanannun ƴaƴan jam'iyyar PDP ne a ƙauyen su na Arosiya, cikin ƙaramar hukumar Maiyama ta jihar Kebbi.

Ya bayyana cewa ba su nemi da a ba su taki, shinkafa, atamfa da kuɗin da jigon APC ɗin ya ba su ba domin su nemo ƙuri'a ga ɗan takarar sa da jam'iyyar sa lokacin zaɓen da ya gabata a jihar.

"Duba da dokar zaɓe, mai shigar da ƙara ya tafka laifin zaɓe." A cewar lauyan waɗanda ake ƙara." A cewarsa.

An fara karanta ƙarar ne a ranar Talata, 2 ga watan Mayu, a gaban babban majistate Adamu Sani.

Sai dai, an ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 15 ga watan Mayu, domin cigaba da shari'a.

Malamin Addini Ya Hango Wani Kuskure a Rantsar Da Bola Tinubu

A wani rahoton na daban kuma, wani malamin addinin ya ce bai kamata a rantsar da Bola Tinubu kan mulki ba.

John Onaiyekan ya ce kuskure ne rantsar da Tinubu, yayin da ake ƙalubalantar nasarar sa a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel