Ana Dab Da Rantsuwa, Malamin Addini Ya Hango Wani Kuskure a Rantsar Da Bola Tinubu

Ana Dab Da Rantsuwa, Malamin Addini Ya Hango Wani Kuskure a Rantsar Da Bola Tinubu

  • Wani babban fasto ya bayyana cewa babu wani hankali a cikin rantsar da Bola Timubu saboda akwai ƙura a kansa
  • Akbishop John Onaiyekan ya ce bai kamata a rantsar da Tinubu ba saboda ana ƙalubalantar masarars a Kotu
  • Faston ya yi kiran da a y wa yadda aƙe.zaɓen garambawul a ƙasar nan saboda gujewa irin wannan

Abuja - Tsohon Akbishop na ɗariƙar Katolika a birnin tarayya Abuja, John Onaiyekan, ya ce babu wani hankali a ce za a rantsar da Bola Tinubu kafin a kammala sauraron ƙararrakin zaɓe.

Ana sa ran a ranar 29 ga watan Mayun 2023, za a rantsar da Bola Tinubu. Sai dai Peter Obi na jam'iyyar Labour Party (LP) da Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙalubalantar nasarar sa a kotu.

Kara karanta wannan

Ziyarar Tinubu Zuwa Rivers: Gwamna Wike Ya Ayyana Ranar Hutu a Jihar Domin Tarbar Zababben Shugaban Kasa

Babban fasto ya hango kuskure a rantsar da Tinubu
Tsohon Akbishop na Abuja, John Onaiyekan Hoto: Channels tv
Asali: Twitter

The Cable tace da ya ke magana a ya yin wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels tv, a ranar Alhamis, Onaiyekan ya ce akwai buƙatar a sake duba kan yadda ake zaɓe a ƙasar nan, inda ya yi nuni da cewa hakan zai samar da shugabanni waɗanda ba su fama da ƙalubale a kotu saboda nasarar su.

Malamin addinin ya ce duk ƴan takarar da ake ƙalubalantar nasarar su a kotu, bai kamata a rantsar da su ba, cewar rahoton Sahara Reporters.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Akwai ƙararraki a kotu waɗanda ba a kammala ba. Shiyasa mu ka samu kan mu cikin wani irin hali. Muna da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa wanda ake ƙalubalantar sa sannan lamarin yana hannun kotu."
"Har yanzu ina jiran kotu ta gaya min wane ne ya lashe zaɓen. Babu wani hankali a ce ana rantsar da mutane waɗanda ake shari'a da su a kotu."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Dalibar Ajin Karshe a Jami'a Ta Mutu Cikin Barci Da Tsakar Dare

"Na san cewa hakan ya faru da wasu gwamnoni, sannan abinda ya biyo baya, ba daɗi ya yi mu su ba. Ina tunanin yakamata mu sake duba kan hanyoyin gudanar da zaɓe, ta yadda za mu samu wanda ya yi nasara za a rantsar wanda kowa zai mara masa baya."

'Yar Majalisa Mace Ta Fito Takarar Kujera Mafi Girma Ta 2 a Majalisa

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa ƴar majalisa mace ta fito takarar mataimakiyar kakakin majalisar wakilai.

Tolulope Akande-Sadipe tace ta shirya tsaf domin neman kujerar idan har.jam'oyyar APC ta kai ta yankin ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel