‘Dan Takaran da Ake Zargi da Yi wa APC Aiki a 2023 Ya Fito Fili Yana Goyon Bayan Tinubu

‘Dan Takaran da Ake Zargi da Yi wa APC Aiki a 2023 Ya Fito Fili Yana Goyon Bayan Tinubu

  • Prince Adewole Adebayo bai da niyyar yi wa Asiwaju Bola Tinubu duk da APC ta doke shi a 2023
  • ‘Dan takaran shugaban kasar ya ce goyon bayan shugaba mai jiran gado ne zai kawowa kasa cigaba
  • Adebayo yana ganin Tinubu ya yi magudi, wannan bai jawo ya tafi kotu ba, ya karbi sakamakon

Abuja - Prince Adewole Adebayo wanda ya tsayawa SDP takara a zaben shugaban kasa da aka yi a Fubrairun nan, ya sallama cewa ya sha kashi.

A ranar Alhamis, Daily Trust ta rahoto cewa Prince Adewole Adebayo ya ba mutanen Najeriya shawara da cewa su goyi bayan Asiwaju Bola Tinubu.

‘Dan takaran ya na so al’umma su marawa Bola Tinubu baya saboda gwamnatinsa ta yi nasara.

Bayanin nan ya fito daga bakin ‘dan siyasar ne a wajen wani taro da Segun Awosanya ya shirya a dalilin sada zumunta na Twitter a jiya.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Abin da Ya Hana Kwankwaso Zuwa Kotu a Kan Zaben Shugaban Kasa

A ra’ayin Prince Adebayo, shugabanci yana farawa ne da zarar hukumar zabe na kasa ta INEC ta sanar da wanda ya lashe zabe, kafin ya zauna a ofis.

Duk da yana da ja a game da yadda zaben 2023 ya kasance, ‘dan takaran na jam’iyyar SDP bai ganin cewa hakan ya kamata ya kawo cikas a mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu
Bola Tinubu dauke da tsintsiya Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

Siyasa ba tare da gaba ba

Abin da hakan ya nuna shi ne wanda aka doke a zaben banan, yana siyasa ne ba da gaba ba.

"Siyasa hanyar zakulo jagorori ne domin samun shugabanci na kwarai. Na sha kashi a zaben. Sannan ina da korafi a game da zaben, kuma na huce.
Idan ana so a rika maganar Najeriya a sahun kasashen da suka yi zarra, Adebayo ya ce ya wajaba a daina siyasar kabilanci, bangaranci da addini.

Kara karanta wannan

Toh fa: Tinubu ya watsar da 'yan APC, ya ce ba dan wani gwamnan PDP ba da ya fadi zabe

Tir da siyasar bambanci

Idan aka samu Musulmi da Musulmi a fadar shugaban kasa, kasa za ta zauna idan sun dace.
Idan aka samu mulkin Musulmi da Kirista, kasar za ta wargaje idan dukkansu ba na kwarai ba ne. Ba batun addini ba ne, abin yana ga mutanen nan ne.”

Rikicin shugabancin majalisa

Ana tunanin Ahmad Lawan da Ovie Omo-Agege su na yakar APC da shugaba mai jiran gado Bola Tinubu ta bayan fage, wani rahoto ya nuna haka.

Kungiyar DCD ta sanar da zababbun Sanatoci da ‘Yan Najeriya cewa sun gano aika-aikar shugabannin majalisa na kawo wanda za a iya juya shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel