Kamfanin IKEDC Ya Rage Kudin Wutar Lantarki Ga Abokan Hulda a Rukunin ‘Band A’

Kamfanin IKEDC Ya Rage Kudin Wutar Lantarki Ga Abokan Hulda a Rukunin ‘Band A’

  • A wani mataki na samar da sauki ga kwastomominsa, kamfanin rarraba wutar lantarki na Ikeja (IKEDC) ya sanar da rage farashin wutar lantarki
  • Kamfanin ya rage kudin ne ga abokan cinikinsa na 'Band A' da ke biyan N225/kWh bayan umarnin hukumar kula da rarraba wutar (NERC)
  • A zantawarmu da Alhaji Bala Ibrahim, mazaunin mazaunin unguwar 'yan majalisu da ke Kaduna, ya ce ragin N19 ba abin ayi murna ba ne

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ikeja ya rage kudin wutar da abokan cinikinsa na 'Band A' ke biya zuwa N206.80/kWh daga N225/kWh da hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta amince.

Kara karanta wannan

Wutan lantarki: Kamfanin KEDCO ya yiwa abokan huldarsa a jihohi 3 albishir

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Ikeja ya rage kudin wuta ga 'yan 'Ban A'
Kamfanin IKEDC ya rage kudin wuta daga N225/kWh zuwa N206.80/kWh ga 'yan 'Band A'. Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Kamfanin IKEDC ya rage kudin wuta

Kakakin IKEDC, Olufadeke Omo-Omorodion, ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Channels a wata sanarwa a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, sabon kudin wutar da aka rage wa abokan cinikin da ke karkashin rukunin 'Band A' zai fara aiki daga Litinin, Mayu 6, 2024.

Abokan cinikin da ke samun wuta ta awanni 20 a rana wadanda har yanzu ake cajarsu N225/Kwh, yanzu za su koma biyan N206.80/KWh, in ji rahoton jaridar Leadership.

"Dalilin rage kudin wutar" - IKEDC

Kamfanin rarraba wutar na IKEDC ya ba abokan ciniki a karkashin 'Band A' tabbacin samun wutar lantarki na sa'o'i 20 zuwa 24 a kullum.

Shawarar rage kudin wutar ya jaddada himmar kamfanin na haɓaka kyakkyawar alakarsa da abokan ciniki da tabbatar da samun wutar lantarki mai araha.

Kara karanta wannan

Tsugune ba ta ƙare ba yayin da NNPCL ta sake korafi kan bashin 2.8trn na cire tallafi

Ko da yake, jaridar The Nation ta ruwaito kamfanin ya bayyana cewa farashin wutar lantarki ga abokan ciniki na Band B, C, D, da E yana nan a yadda yake, ba a canza ba.

"Ba abin murna ba ne" - Alhaji Bala

Alhaji Bala Ibrahim, mazaunin unguwar 'yan majalisu da ke Kaduna, a zantawarsa da wakilinmu ya ce wannan ragin na N19 ba abin murna ba ne.

Alhaji Bala ya yi nuni da cewa, gwamnati ta kara kudin daga N66 zuwa N225, karin N159, kenan duk da an rage N19 har yanzu karin N140 yana nan.

"Ko da ace muna samun wutar awa 20 a rana, bai kamata ayi karin kudin ya yi yawa haka ba, wannan matsin tattalin ya shafi mai kudi kamar yadda ya shafi talaka."

Ya yi kira ga gwamnati da ta sake yin duba kan wannan karin kudin da ta yi yana mai ta'allaka dalilinsa da tabarbarewar kasuwanci, durkushewar Naira da sauran su.

Kara karanta wannan

"An yi watsi da su": Jigon APC ya magantu kan halin da El-Rufai da Yahaya Bello ke ciki

NERC ta takaita kai wuta waje

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito hukumar da ke kula da rarraba wutar lantarki ta Najeriya (NERC ) ta takaita kai wutar lantarki zuwa Nijar, Mali da Togo.

Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya ke bin kasashen uku bashin sama da Naira biliyan 130, da kuma kokarin NERC na daidaita wutar a cikin gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel