Kwamishinan Zaben Adamawa: Ban Yi Danasanin Ayyana Binani a Matsayin Wacce Ta Lashe Zabe Ba

Kwamishinan Zaben Adamawa: Ban Yi Danasanin Ayyana Binani a Matsayin Wacce Ta Lashe Zabe Ba

  • Kwamishinan zabe na jihar Adamawa wanda aka dakatar, ya ce bai yi nadamar bayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar ba
  • Hudu Ari ya ce ya bi duk wata doka da ta dace kafin ayyana yar takarar gwamnan ta jam'iyyar APC a matsayin zababbiyar gwamna
  • Ya kuma yi rantsuwa da Allah cewar bai karbi biliyan biyu daga hannun kowa ba kamar yadda aka ta yayatawa

Kwamishinan zabe na Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa-Ari, ya ce bai yi nadamar ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna na ranar 15 ga watan Afrilun ba a jihar, jaridar The Cable ta rahoto.

Yunusa-Ari ya haddasa cece-kuce bayan ya bayyana Aisha Binani Dahiru ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wacce ta lashe zabe yayin da ba a kammala tattara sakamako ba.

Kara karanta wannan

Bayan Dogon Lokaci, Gaskiya Ta Bayyana Kan Baiwa Kwamishinan Zaben Adamawa Cin Hancin N2bn

Dakataccen kwamishinan zaben Adamawa, Hudu Yunusa-Ari
Kwamishinan Zaben Adamawa: Ban Yi Danasanin Ayyana Binani a Matsayin Wacce Ta Lashe Zabe Ba Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta soke sanarwar da ya yi sannan ta sammaci kwamishinan zaben zuwa hedkwatarta da ke Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da kwamishinan zaben na Adamawa a ranar 20 ga watan Afrilu har zuwa lokacin da yan sanda za su kammala bincike.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwana daya bayan nan, sai INEC ta ce bata san inda Yunusa-Ari yake ba.

Da yake zantawa da sashin Hausa na BBC a ranar Talata, Yunusa-Ari ya ce babu wanda ya bashi kudi don bayar da sanarwar.

Ban taba shiya yar buya ba, kwamishinan zaben Adamawa da aka dakatar

Dakataccen kwamishinan ya ce bai taba shiga yar buya ba, yana mai cewar zai amsa gayyatar yan sanda.

Yunusa-Ari ya ce:

"Ban tambayi Binani da Fintiri ko sisin kwabo ba. Ya sabama addinina karbar kudi daga wajen wani don taimaka masa wajen yin wani abu kuma na rantse da Allah, ikirarin cewa an bani naira biliyan biyu zargi ne mara tushe da jita-jita.

Kara karanta wannan

Atiku ne ya lashe zabe: PDP ta caccaki ministan Buhari, ta tono barnar APC

"Ina zan kai naira biliyan 2? Na gani a soshiyal midiya cewa an bani biliyan N2.
"Ban yi nadamar bayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zaben ba. Duk abun da ka yi daidai da doka, ba za ka yi nadama ba.
"Na rubuta wata wasika zuwa ga INEC wanda suka ce ba za su yarda ba - amma na tabbata sun yarda da shi kuma gayyatar da yan sanda suka yi mani dole ne na amsa ta.
"Ban taba shiga yar buya ba. Zan amsa gayyatar yan sanda."

Kwamishinan zaben Adamawa: Yan sanda sun kama hudu-Ari

A gefe guda, mun ji a baya cewa rundunar yan sandan Najeriya ta cika hannu da tsohon kwamishinan zaben jihar Adamawa, Yunusa Hudu-Ari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel